Wani matashi ya kashe makwabciyarsa saboda ta tambaye shi ranar da zai yi aure

Wani matashi ya kashe makwabciyarsa saboda ta tambaye shi ranar da zai yi aure

Hakika ko da ace tambayar 'yaushe za ka yi aure' ta fito daga bakin mutanen da kake jin nauyinsu, tana da sosa zuciya, musamman idan suka ci gaba da yi maka irin tambayar duk lokacin da kuka hadu. Ku dauki misalin hakan daga wannan matashin wanda ya kashe makwabciyarsa saboda yawaita yi masa irin wannan tambaya.

Rahotanni sun bayyana cewa wani matashi mai shekaru 28, Faiz Nurdin, da ke da zama a Kampurng Pasir Jonge, Indonesia, ya kashe wata makwabciyarsa mai suna Aisyah. Faiz ya kashe makwabciyar ta sa saboda yawan tambayarsa 'yaushe za ka yi aure?'

Mazaunar unguwar, Astro Awani da Sinar Harian, sun bayyana cewa Faiz na zaune a kofar gidansa a lokacin da makwabciyar ta sa ta zo shigewa ta kusa da shi, inda ta yi masa magana.

KARANTA WANNAN: Babbar nasara: Yadda aka gano hanyar magance cutar kanjamau

Wani matashi ya kashe makwabciyarsa saboda ta tambaye shi ranar da zai yi aure
Wani matashi ya kashe makwabciyarsa saboda ta tambaye shi ranar da zai yi aure
Asali: Twitter

Kamar yadda wata majiya daga rundunar 'yan sanda ta yankin ta bayyana cewa: "Wanda ake zargin ya labarta cewa matar ta ce da shi, 'ka hanzarta yin aure, kowa ya yi aure, kai me ya sa ka kasa yin aure?' Wadannan kalaman sun bata ran wanda ake zargin,"

Rahotanni daga Buzzflare ya bayyana cewa Faiz ya ziyarci makwabciyar ta sa har cikin gidanta, inda ya bi ta cikin daki tare da wurga ta saman gado, ya yi amfani da hannunsa duk da yunkurin matar na ture shi amma ya shaketa har lahira.

Bayan aikata wannan danyen aiki, Faiz ya yi nasarar tserewa zuwa garin Kalideres da ke Jakarta amma jami'an tsaro suka samu damar cafke shi bayan da suka harbe shi a kafa.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin zai fuskanci hukuncin daurin rai-da-rai idan har aka tabbatar shi ne ya aikata kisan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel