Tauye hakki: Ma'aikata sun yiwa Gwamna Amosun ihu, sun kunyata shi

Tauye hakki: Ma'aikata sun yiwa Gwamna Amosun ihu, sun kunyata shi

Dubban ma'aikatan jihar Ogun da ke cike da fushi ne suka gudanar da zanga-zangan rashin amincewa da rashin biyan su hakokinsu da gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun ya ke yi inda suka rika masa ihu tare da furta kalamai masara dadi a gareshi a ranar Talata.

Amosun dai ya yana cikin taro ne tare da shugaban kungiyar kwadago na kasa NLC, Ayuba Wabba da wasu shugabanin kungiyar amma sai ya yanke taron bayan an sanar da shi cewa fusatattun ma'aikatan sun hanyarsu ta zuwa Oke-Mosan inda ofishinsa ya ke.

Sai dai duk da hakan, ma'aikatan sun cimma gwamnan a yayin ta ya ke kokarin tserewa a cikin motarsa inda suka fara yi masa ihu tare da furta kalamu marasa dadi a gare shi.

Rashin kyautatawa ma'aikata: An yiwa gwamna Amosun ihu, an kunyata shi
Rashin kyautatawa ma'aikata: An yiwa gwamna Amosun ihu, an kunyata shi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Radadin kaye: Masoyin Atiku ya hana wani mabaraci sadaka (Bidiyo)

Ma'aikatan sun shawarci Wabba da sauran shugabanin NLC da ke zaman sulhu da gwamnan suyi taka tsan-tsan da shi domin a cewarsu, Gwamna Amosun ya saba daukan alkawari amma ba zai cika ba.

Wabba, wanda ya fito daga wurin taron domin ya kwantar wa ma'aikatan hankulansu ya ce sun fara tattaunawa da gwamnan bisa muhimman matsaloli hudu da ma'aikatan jihar ke fuskanta kuma suna da tabbacin gwamnan sai magance matsalolin.

Shugaban na NLC ya ce daya daga cikin matsalolin shine mayar da shugaban NLC na jihar da aka tsige tun shekarar guda da ta gabata, Akeem Ambali kan kujerarsa. Ya sanar da cewa an mayar da Ambali kan kujerarsa kuma ya kara da cewa ziyarsu jihar ba ta alaka da siyasa.

Ya ce gwamnan zai saka hannu a kan yarjejeniya na cewar zai magance matsalolin ma'aikatan jihar da suka hada da biyan albashi, biyan kudaden da ake cirewa daga albashin wasu, kudin fansho, albashim ma'aikatan kwalejin Ilimi na Tai Solarin da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel