'Yan bindiga sunyi awon gaba da wasu malaman addini biyu a Filato

'Yan bindiga sunyi awon gaba da wasu malaman addini biyu a Filato

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sunyi awon gaba da wani faston cocin ERCC da ke karamar hukumar Quaapan na jihar Filato mai suna Rev. Thomas Ashaku.

An gano cewa an sace faston ne da sakataren cocin mai suna Mr. Ezikiel Agwadu yayin wata addu'a ta musamman da cocin ta shirya a unguwar Namu.

Anyi yunkurin tuntunbar jami'an hulda da jama'a na 'yan sanda na jihar, Mr Tyopev Teena sai dai bai amsa wayarsa ba amma shugaban kungiyar Kirista CAN na garin Quaapan, Rev. Isaac Tali ya tabbatarwa Punch sace malaman addinin biyu a ranar Talata a Jos.

DUBA WANNAN: Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi

An sace malaman addini biyu yayin gudanar da addu'ar cikin dare
An sace malaman addini biyu yayin gudanar da addu'ar cikin dare
Asali: Twitter

A cewarsa, lamarin ya faru ne a daren Juma'a amma bai samu labari ba har sai safiyar ranar Talata.

Tali ya ce, "Yanzu aka sanar da ni abinda ya faru. Shugaban matasa na CAN na Arewacin Jos na ya kira ni a waya domin ya sanar da ni abinda ke faruwa kuma nayi bincike na gano abin gaskiya ne.

"An ce 'yan bindigan sun kai farmaki harabar cocin ne amma suka tsince shugabanin cocin biyu kawai ba su taba kowa ba. Wannan abin mamaki ne kuma bai dace a bari hakan na faruwa ba."

Ciyaman din shiyya na CAN a unguwar ya ce an sanar da 'yan sanda abinda ya faru kuma 'yan bindigan da suka sace malaman addinin sun nemi a biya su kudin fansa kafin su sako su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel