Bakin jinin PDP, zargin sata da sauran dalilin da su ka sa Saraki ya sha kasa

Bakin jinin PDP, zargin sata da sauran dalilin da su ka sa Saraki ya sha kasa

A zaben ‘yan majalisu da shugaban kasa da aka yi, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, yana cikin manyan wadanda su ka sha kashi a zaben bana. PDP ta sha kashi ne ko ta ina a hannin jam’iyyar APC a Jihar ta Kwara.

Bakin jinin PDP, zargin sata da sauran dalilin da su ka sa Saraki ya sha kasa
Bukola Saraki ya rasa kujerar Sanatan sa wajen Jam’iyyar APC
Asali: Depositphotos

Premium Times ta kawo wasu dalilan da su Bukola Saraki ya rasa tikitin sa na Sanata a karkashin jam’iyyar PDP. Saraki ya dade yana juya akalar siyasar Kwara tun Mahaifin sa yana da rai a Duniya.

Ga kadan daga cikin wadannan dalilai:

1. Rashin albashi

Rashin biyan albashin ma’aikata a jihar Kwara da gwamnatin jihar Kwara ba tayi yana cikin manyan abubuwan da su ka sa Bukola Saraki ya sha kasa a zaben bana. Ana tunanin cewa har yanzu Sanatan ne yake juya akalar gwamnatin Kwara.

2. Sauya-sheka

Barin APC da Bukola Saraki yayi zuwa jam’iyyar PDP tare da gwamna Abdulfatahi Ahmed da wasu ‘Yan majalisun jihar yana cikin abin da ya kara jagwalgwala shugaban majalisar lissafi. Wannan ya ba APC damar tika Saraki da mutanen sa da kasa.

KU KARANTA: Ana rarrashin Atiku ya fasa zuwa Kotu a game da zaben 2019

3. Karfin Gwamnatin sama

Tun fil azal dai Bukola Saraki ya kan yi amfani ne da karfin iko na gwamnatin tarayya. Wannan karo fito-na-fito da yayi da gwamnati mai-ci ta Buhari ba tayi masa rana ba. A 2015 dai, Saraki ya tsere daga PDP bayan ya fahimci Jonathan ya kai kasa.

4. Zargin satar dukiyar Talakawa

Bukola Saraki yana da kashi a jikin sa na zargin da aka rataya masa na sace kudin jama’a; daga badakalar majalisa, zuwa handame baitul malin jihar Kwara da kuma rusa wani banki, Ana kuma zargin tsohon gwamnan da hada albashi biyu a lokaci guda.

5. Kururuwar O to ge

Mutanen APC sun hurowa Bukola Saraki wuta a wannan karo da kiran O to ge (Watau ya isa haka!). Jama’a sun yi wa gidan su Saraki bore bayan sun dade su na mulkar jihar. wannan yayi tasiri wajen ganin APC ta samu nasara a zaben 2019.

Sauran dalilan da su ka sa Saraki ya rasa kujerar sa, sun hada da yadda aka shigo da addini cikin harkar siyasa da kuma juyawa shugaban majalisar baya da manyan ‘yan siyasa musamman na cikin Garin Ilorin da kewayen jihar su kayi a wannan karo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel