An gano yankin da APC ke son bawa kujerun shugabannin majalisa

An gano yankin da APC ke son bawa kujerun shugabannin majalisa

Akwai kwararan alamu da ke nuna cewar jam’iyyar APC mai mulki na son mayar da kujerar shugaban majalisaar dattijai zuwa arewa sannan ta mika kujerar shugaban majalisar wakilai zuwa yankin kudu.

Yanzu haka jam’iyyar APC ke da ma fi rinjayen mambobi a majalisar dattijai da ta wakilai. APC na da sanatoci 64 da mambobin majalisar wakilai fiye da 200.

Wasu ma su ruwa da tsaki a tafiyar da harkokin jam’iyyar APC na kulle-kullen ganin an mika kujerar shugaban majalisar dattijai zuwa yankin arewa, musamman yankin arewa maso gabas, sannan a bawa yankin kudu, musamman kudu maso yamma, kujerar shugaban majalisar wakilai.

Legit.ng ta fahimci cewar ma su ruwa da tsakin na son a bawa yankin kudu maso kudu kujerar mataimakin shugaban majalisar dattijai, sannan a bawa yankin arewa maso ko arewa ta tsakiya kujerar mataimakin shugaban majalisar wakilai.

An gano yankin da APC ke son bawa kujerun shugabannin majalisa
Shugabannin majalisa ma su barin gado
Asali: Depositphotos

Tuni sanatoci uku daga yankin arewa maso gabas; Sanata Ahmed Lawan (Yobe), Sanata Ali Ndume (Borno), Sanata Danjuma Goje (Gombe), da sanata daya daga yankin arewa ta tsakiya; Sanata Abdullahi Adamu (Nasarawa), sun fara yakin neman zama shugaban majalisar dattijai.

A bangaren majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila (Lagos), Mohammed Tahir Monguno (Borno), da Abdulrazak Namdas (Adamawa) sun nuna sha’awar yin takarar neman jagorantar majalisar wakilai.

DUBA WANNAN: Zabe: Kotu ta kori karar da PDP ta shigar da gwamnan APC

Wasu mambobin da su ka nuna sha’awar shugabancin majalisar wakilai su ne; Ahmed Idris Wase (Filato), Umar Bago (Neja), da Babangida Ibrahim (Katsina).

Abdulaziz Yari, gwamnan jihar Zamfara mai baring ado, ya nuna sha’awar sa ta son zama mataimakin shugaban majalisar dattijai.

Kazalika, ‘yan majalisar wakilai biyu daga jihar Kano; Abdulrahman Kawu Sumaila da Aminu Suleiman Goro, sun nuna sha’awar yin takarar kujerar mataimakin shugaban majalisar wakilai.

Tuni Gbajabiamila da Kawu sun fara tuntubar mambobin majalisar domin neman goyon bayan su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel