APC ta soke ziyarar da Buhari zai kai zuwa wasu jihohin PDP 5

APC ta soke ziyarar da Buhari zai kai zuwa wasu jihohin PDP 5

Akwai yiwuwar jam'iyyar APC mai mulki ta dage shirin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na kai ziyara wasu johihi 5 da ake ganin jam'iyyar PDP ne ke da rinjaye domin ya janyo hankalin masu zabe gabanin zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

An gano cewa an soke ziyarar da shugaban kasar zai kai zuwa jihohin Delta, Akwa Ibom, Sokoto, Kwara da Taraba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wata jihar da aka kara cikin jihohin da shuagaban kasa zai kai ziyarar itace jihar Imo. Duk da cewa jam'iyyar APC ne ke mulki ajihar, ana ta samun rashin jituwa tsakanin gwamnan jihar da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Radadin kaye: Masoyin Atiku ya hana wani mabaraci sadaka (Bidiyo)

APC ta soke ziyarar da Buhari zai kai zuwa wasu jihohin PDP 5
APC ta soke ziyarar da Buhari zai kai zuwa wasu jihohin PDP 5
Asali: UGC

A maimakon shugaba Muhammadu Buhari, za a aike da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo domin ta tafi jihohin Delta da Akwa Ibom da ake ganin sune jihohin da za su sanya APC karbuwa a yankin Neja Delta.

A jiya ne aka gano cewa shugaban kasar ya fasa kai ziyarar zuwa jihohin PDP na Arewa wato Kwara, Sokoto da Taraba.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa a jiya ta tabbatar da cewa an soke ziyarar da shugabna kasa zai kai jihar Imo. 'Yan jarida ba su gano dalilin da yasa aka soke ziyarar zuwa jihohin biyar ba.

Wani jigo a APC da aka tuntuba ya ce bai san dalilin da yasa aka soke ziyarar ba. Kazalika, fadar shugaban kasa ba ta amsa sakon kar ta kwana da kirar waya da akayi mata ba a yayin rubuta wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel