Yanzu Yanzu: An gurfanar da Dino Melaye yan kwanaki bayan lashe zabensa

Yanzu Yanzu: An gurfanar da Dino Melaye yan kwanaki bayan lashe zabensa

- Hukumar yan sanda ta gurfanar da Sanata Dino Melaye a gaban babbar kotun tarayya da ke Apo, Abuja a yau

- Melaye dai na fusaknatar tuhume-tuhume shida, ciki harda na yunkurin kashe kansa

- Kwanan nan ne dai sanatan ya sake lashe kujerar dan majalisar dattawan kasar a yankin Kogi ta yamma

Yan kwanaki bayan nasararsa a zabe, hukumar yan sanda ta gurfanar da Sanata Dino Melaye a gaban babbar kotun tarayya da ke Apo, Abuja a ranar Talata, 5 ga watan Maris kan tuhume-tuhume shida, ciki harda na yunkurin kashe kansa.

Daga wani rukuni na tuhumar, an zargi Sanata Melaye da yunkurin tserewa daga inda aka tsare shi.

Yanzu Yanzu: An gurfanar da Dino Melaye yan kwanaki bayan lashe zabensa
Yanzu Yanzu: An gurfanar da Dino Melaye yan kwanaki bayan lashe zabensa
Asali: UGC

Melaye wanda kwanan nan ya sake lashe kujerar satana mai wakiltan Kogi ta yamma na fuskantar zargin lalata kayayyakin yan sanda.

KU KARANTA KUMA: Babu wani shiri da ake na tsige Sultan na Sokoto- APC

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Sanata Melaye ya karyata aikata dukkanin laifuffukan da ake tuhumarsa a kai.

Rahoton ya kawo inda Justis Sylvanus Oriji yayi bayanin cewa yana sane da cewar kotu ta bayar da belin Melaye a lokacin da aka gurfanar dashi a gabansa a ranar 25 ga watan Yulin 2018, akan wannan tuhume-tuhumen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel