Kwamitin shugaban kasa ya bukaci APC ta gaggauta janye matakin korar Okorocha

Kwamitin shugaban kasa ya bukaci APC ta gaggauta janye matakin korar Okorocha

- Kwamitin shugaban kasa PSC ya bukaci kwamitin gudanarwa na APC da ya gaggauta janye matakin da ya dauka na korar Okorocha

- Kwamitin ya bayyana bukatarta na son a baiwa dan shiyyar Kudu maso Gabas kujerar shugaban majalisar dattijai duba da irin goyon bayan da suka baiwa shugaban kasar

- Kwamitin ya ce an kulla shirin dakatar da manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ne domin hanawa kabilar Igbo shugabancin Nigeria a shekarar 2023

Kwamitin goyon bayan shugaban kasa PSC, na shiyyar Kudu maso Gabas, ta baiwa kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC karkashin jam'iyyar APC, awanni 48 da ta janye matakin da ta dauka na dakatar da gwamnan jihar Imo, Owelle Rochas Okorocha daga jam'iyyar.

Kwamitin ya kuma yi tsokaci kan kujerar shugaban majalisar dattijai da ta ke so a baiwa dan shiyyar Kudu maso Gabas duba da irin goyon bayan da suka baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabreru.

KARANTA WANNAN: 'An yi mun fashi da makami' - Shehu Sani ya bayyana dalilin faduwarsa zabe

Kwamitin shugaban kasa ya bukaci APC ta gaggauta janye matakin korar Okorocha
Kwamitin shugaban kasa ya bukaci APC ta gaggauta janye matakin korar Okorocha
Asali: UGC

A wani taron manema labarai a garin Owerri kan nazarin zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya, kwamitin ya yi nuni da cewa dakatar da manyan masu ruwa da tsaki da kuma masu daukar nauyin harkokin jam'iyyar kamar irinsu Okorocha, ba zai haifarwa NWC na APC d'a mai ido ba, inda ta yi ikirarin daukar mataki ma damar ba a janye dakatarwar ba.

Taron manema labaran ya samu halartar manyan shuwagabannin kwamitin, inda manyan shuwagabannin suka gudanar da jawabai, kamar daraktan harkokin cikin kwamitin na Kudu maso Gabas; Robert Ngwu, shugaban lauyoyi masu kare kwamitin na kasa; Ejikeme Ugwu da kuma daraktan harkokin siyasa; Kwamred Maxwel Okoye.

Kwamitin ya ce an kulla shirin dakatar da manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ne domin hanawa kabilar Igbo shugabancin Nigeria a shekarar 2023, tunda ana sane da cewa Okorocha na daga cikin manyan wadanda za su tsaya takara a wannan shekarar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel