Zaben 2019: PDP za ta kai ƙarar APC wajen Majalisar dinkin Duniya

Zaben 2019: PDP za ta kai ƙarar APC wajen Majalisar dinkin Duniya

- Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayar da sanarwar shirye-shiryen ta na aikewa da rubutacciyar ƙara zuwa ga Majalisar Dinkin Duniya dangane da babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

- PDP ta yi zargin cewa jam'iyyar APC ta ribaci dakarun soji wajen aikata miyagun ababe na murdiya da magudin zabe domin rinjayar da nasara a gare ta.

- Jam'iyyar za ta yi ƙarar rawar da dakarun sojin Najeriya suka taka da yayin babban zaben kasa wajen cibiyoyin dimokuradiyya na duniya.

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ta bayyana shirye-shiryen ta na aikewa da rubutacciyar ƙara zuwa ga Majalisar dinkin duniya dangane da yadda dakarun sojin Najeriya suka taka rawar gani wajen aikata miyagun ababe yayin babban zabe.

Kakakin jam'iyyar PDP na kasa; Mista Kola Ologbondiyan
Kakakin jam'iyyar PDP na kasa; Mista Kola Ologbondiyan
Asali: UGC

Bayan kammala tuntube-tuntube, jam'iyyar PDP ta ce ta yanke shawarar mika korafin ta zuwa majalisar dinkin duniya dangane da yadda rundunar dakarun sojin Najeriya ta taka rawar gani wajen kulla tuggu da miyagun ababe na magudi da rashin adalci yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.

Kakakin jam'iyyar PDP na kasa, Mista Kola Ologbondiyan, shine ya bayar da shaidar hakan a jiya Litinin yayin ganawa da manema labarai bayan kammala taron jiga-jigan jam'iyyar da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Ya ke cewa, jam'iyyar PDP ba kuma za ta gaza ba wajen shigar da ƙara zuwa ga cibiyoyi da hukumomin dimokuradiyya na duniya dangane da yadda rundunar sojin Najeriya ta taka rawar gani wajen aikata miyagun ababe da dungushe gami da rashin gaskiya domin rinjayar da nasara zuwa ga jam'iyyar APC a yayin babban zabe.

KARANTA KUMA: Buhari na goyon bayan mika wa 'yan Kabilar Ibo mulki a 2023 - Okwara

Kamar yadda Mista Ologbondiyan ya bayyana, jam'iyyar PDP na ci gaba da zaman dar-dar dangane da zargi kan yunkurin gwamnatin APC na amfani da dakarun soji wajen murdiya gami da aikata miyagun ababe a Kudancin kasar nan yayin zaben gwamnoni da za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Kazalika kakakin jam'iyyar yayin yunkurin jaddada matsaya da kuma tunatarwa, ya ce dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar, Atiku Abubakar, ba zai gaza ba wajen neman yakkin sa a shari'ance dangane da rashin adalci da ya auku yayin zaben kujerar shugaban kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel