'An yi mun fashi da makami' - Shehu Sani ya bayyana dalilin faduwarsa zabe

'An yi mun fashi da makami' - Shehu Sani ya bayyana dalilin faduwarsa zabe

- Sanata Shehu Sani, ya bayyana dalilin da ya sa ya fadi zaben mazabarsa, a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da ya gudana a ranar Asabar 23 ga watan Fabreru

- Sanata Sani, ya alakanta faduwarsa zaben akan irin magudin da aka tafka a zabukan

- Dan majalisar ya yi Allah-wadai da sakamakon zaben mako daya bayan da aka sanar da faduwarsa, wanda ya sa ya gaza samun damar zarcewa majalisar dattijan

Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai, Sanata Shehu Sani, ya bayyana dalilin da ya sa ya fadi zaben mazabarsa, a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da ya gudana a ranar Asabar 23 ga watan Fabreru.

Sanata Sani, wanda kasance bako a cikin wani shirin siyasa na gidan talabijin din Channels, ya alakanta faduwarsa zaben akan irin magudin da aka tafka a zabukan.

"Ba na jin na fadi wannan zaben saboda ya kan zama abu mai wuya ka fadi zabe idan har an gudanar da sahihi, wanda babu magudi a ciki," a cewar dan takarar jam'iyyar na PRP, a tattaunawarsa cikin shirin da ya gudana a ranar Litinin.

KARANTA WANNAN: Akwa Ibom: Zamu tabbata mun dawo da martabarmu a zaben ranar Asabar - Buhari

'An yi mun fashi da makami' - Shehu Sani ya bayyana dalilin faduwarsa zabe
'An yi mun fashi da makami' - Shehu Sani ya bayyana dalilin faduwarsa zabe
Asali: UGC

Ya kara da cewa, "Idan har fashi da makami ne, to ko dai kai ne ka yi fashin, ko kuma kai ne aka yiwa, a wannan bagiren, ina ga ni ne aka yiwa fashi da makami."

Dan majalisar ya yi Allah-wadai da sakamakon zaben mako daya bayan da aka sanar da faduwarsa, wanda ya sa ya gaza samun damar zarcewa majalisar dattijan.

Rahotanni sun bayyana cewa Shehu Sani ya zo na biyu bayan dan takarar jam'iyyar APC, Uba Sanni, wanda ya lashe zaben da kuma dan takarar jam'iyyar PDP,. Lawal Adamu wanda ya zo na biyu.

Amma Sanata Sani ya ki amincewa da sakamakon wannan zabe yana mai ikirarin cewa an tafka magudin zaben, inda ya yi ikirarin cewa akwai rumfunan zaben da ba a kai masu takardun kad'a kuri'a na kujerar sanatoci ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel