Dalilai 4 da suka sa Atiku shan kashi a zaben kasar

Dalilai 4 da suka sa Atiku shan kashi a zaben kasar

Batun zaben Shugaban kasa dai ya kusan ya zamo tsohon labari a Najeriya domin dai hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta dade da sanar dawanda ya lashe zaben.

Tun a ranar Laraba, 27 ga watan Fabrairu hukumar zaben ta sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda yayi nasara a zaben kasar da aka gudanar.

Sai dai har yanzu babban abokin adawarsa kuma dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar bai saduda ba domin yaki amincewa da sakamakon.

Dalilai 4 da suka sa Atiku shan kashi a zaben kasar
Dalilai 4 da suka sa Atiku shan kashi a zaben kasar
Asali: Facebook

A halin yanzu yana shirin garzayawa kotu domin neman hakkinsa bayan ya zargi jam’iyya mai mulki da yin magudi.

Masana siyasa na alakanta wasu dalilai hudu da suke ganin sune suka yi sanadiyar faduwa Atiku a zaben.

KU KARANTA KUMA: Yan kwanaki kafin zaben Gwamna: Kansilolin PDP 15 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kwara

Ga dalilan kamar haka:

1. Ikirarin sayar da NNPC

Mutane da daman a zargin ikirarin da tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yin a siyar da kamfanin man Najeriya idan har yayi nasarar zabe a lokacin da yake yakin neman zabe a matsayin abunda ya hana mutane zabarsa.

Ana ganin kamar subutar baki ce Atiku ya yi da fadin wadannan kalamai amma dan takarar yana sane ya fadi hakan.

Matsalar ita ce bai fito fili ya yi wa 'yan kasar bayanin me yasa zai sayar da kamfanin ba.

Wadannan kalaman da ya yi 'yan jam'iyyar APC sun yi amfani da su domin kushe Atiku Abubakar wajen yakin neman zabe kuma 'yan kasar sun amince da hakan.

Abin da dan Najeriya yake kallo shi ne idan an sayar da kamfanin mai na kasar kudin mai zai karu kuma a ganinsa ita kadai ce kadarar da ta rage da yake amfana da ita.

2. Zargin cin hanci da rashawa

Har yanzu dai ana yiwa dan takarar na PDP kallon mutum da ke dauke da guntun kashi a makale a tsuliyarsa.

Hatta tsohon ubangidansa, Obasanjo ya ito karara ya bayyana shi a matsayin wanda ya aikata rashawa kafin daga bisani suka dinke.

Don haka mutane ke tsoron damka amanar kasar a hannunsa ta hanyar zabarsa ya zamo jagoran kasar.

3. Ikirarin azurta abokansa da 'yan uwansa

Wani abu da Atku ya dauka kamar da wasa ya zama babbar matsala a gare shi shi ne batun da ya yi na cewa zai azurta abokansa da 'yan uwansa.

Domin ya ce idan ya ci zabe zai azurta su, kuma kalaman sun zamo abin da aka yi amfani da su domin kayar da shi a lokacin zabe.

Akasarin 'yan kasar sun tsorata da wadannan kalamai na Atiku domin suna ganin cewa kamar Allah ne ya matse bakinsa ya fadi abin da zai yi idan ya samu nasarar lashe zabe.

4. Guguwar Buhari

Guguwar Buhari kalma ce da ta samo asali tun 2011 a Najeriya a lokacin da shugaban ya fara takara a jam'iyyar CPC.

A Najeriya an yi itifakin cewa babu wani dan takara a tarihin kasar da yake tara jama'a da kuma yake da goyon bayan jama'a kamar Shugaba Buhari.

A 2011 duk da cewa Shugaba Buhari bai samu mulki ba, jam'iyyarsa ta CPC ta ciwo kujeru da dama a fadin kasar, sai kuma a 2015 guguwar ta shugaban kasar ta lashe kujeru kamar wutar daji.

'Yan kasar na ganin kwatanta Buhari da wani dan takara a wannan lokaci abu ne mai wahala sakamakon irin farin jinin da Allah ya bashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel