Buhari na goyon bayan mika wa 'yan Kabilar Ibo mulki a 2023 - Okwara

Buhari na goyon bayan mika wa 'yan Kabilar Ibo mulki a 2023 - Okwara

- Wani jigo na jam'iyyar APC, Cif Livinus Okwara, ya ce yankin Kudu maso Gabashin kasar nan bai taba samar da shugaban kasa ba a tarihin Najeriya

- Okwara ya ce kasancewar Buhari adalin shugaba ba zai gaza ba wajen goyon bayan mika wa 'yan kabilar Ibo akalar jagorancin kasar nan a 2023

- Jigon na APC ya nemi 'yan siyasar yankin Kudu maso Gabashin Najeriya da su hada kawunan su wuri guda domin cin gajiyar kujerar Buhari a 2023

Wani jigo na jam'iyyar APC, Cif Livinus Okwara, cikin bayyana aminci da kuma kyautata yakinin sa, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai gaza ba wajen goyon mika akalar jagorancin kasar nan a hannun 'yan kabilar Ibo a 2023.

Buhari na goyon bayan mika wa 'yan Kabilar Ibo mulki a 2023 - Okwara
Buhari na goyon bayan mika wa 'yan Kabilar Ibo mulki a 2023 - Okwara
Asali: UGC

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Cif Okwara ya ce shugaban kasa Buhari ba zai kosa ba wajen mika akalar jagorancin kasar nan a hannun 'yan kabilar Ibo duk da rashin samun goyon bayan yankin su na Kudu maso Gabashin kasar nan yayin babban zaben kasa na 2019.

Cif Okwara ya ke cewa, kasancewar shugaban kasa Buhari adalin jagora, a shekarar 2023 zai jajirce wajen ganin akalar jagorancin kasar nan ta koma hannun 'yan kabilar Ibo da tarihi ya tabbatar yankin su na Kudu maso Gabashin Najeriya bai taba samar da shugaban kasa ba.

Yayin ci gaba da ganawa da manema labarai na jaridar The Nation, Cif Okwara ya yi kira ga 'yan siyasar yankin Kudu maso Gabashin kasar nan da su hada kawunan su tare da kasancewa tsintsiya madauri daya wajen cin gajiyar kujerar shugaba Buhari a 2023.

KARANTA KUMA: SERAP ta maka gwamnatin Najeriya gaban Kuliya kan muzgunawa 'yan jarida

Ya kuma kalubalanci kungiyar zamantakewa da al'adun kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo, dangane da gazawar ta wajen kare martabar al'ummar yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, inda ya ce ba bu abinda ya kamata a halin yanzu face a yi watsi da ita.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, kungiyar Ohanaeze Ndigbo reshen jihar Legas, ta bayyana aminci gami da goyon baya kan dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel