Akwa Ibom: Zamu tabbata mun dawo da martabarmu a zaben ranar Asabar - Buhari

Akwa Ibom: Zamu tabbata mun dawo da martabarmu a zaben ranar Asabar - Buhari

- Shugaba Buhari ya ce zasu tabbata sun dawo da martabar su kan kuri'un al'ummar jihar Akwa Ibom da aka yi zargin an sace a zabukan ranar 23 ga watan Fabreru

- Buhari ya koka kan babban rashin da APC ta yi, ta yadda Sanata Godswill Akpabio ya gaza samun nasarar komawa majalisar dattijai

- Ya yi zargin cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ce ta yi masa da al'ummar jihar fashi da makamin nasarar da suka samu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zasu tabbata sun dawo da martabar su kan kuri'un al'ummar jihar Akwa Ibom da aka yi zargin an sace a zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabreru.

Buhari ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da al'umma da ya gudana a Uyo domin godewa al'ummar jihar bisa namijin kokarinsu na fitowa kwansu da kwarkwatarsu, tare da zaben jam'iyyar APC a babban zaben kasar da ya gudana.

Shugaban kasa Buhari, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya karfafawa al'ummar jihar guiwa, kan 'su kasa su tsare kuri'unsu' a zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki da za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris, 2019.

KARANTA WANNAN: Madallah: Ayade ya kaddamar da ma'aikatar samar da tsinken sakucen hakora a Cross Rivers

Akwa Ibom: Zamu tabbata mun dawo da martabarmu a zaben ranar Asabar - Buhari
Akwa Ibom: Zamu tabbata mun dawo da martabarmu a zaben ranar Asabar - Buhari
Asali: UGC

Ya koka kan babban rashin da APC ta yi, ta yadda Sanata Godswill Akpabio ya gaza samun nasarar komawa majalisar dattijan duk da irin kaurin sunan da ya yi a jihar.

Ya yi zargin cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ce ta yi masa da al'ummar jihar fashi da makamin nasarar da suka samu.

Ya baiwa al'ummar jihar Akwa Ibom tabbacin cewa za a magance dukkanin matsalolin da aka samu a zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya gabanin zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel