Yanzu-yanzu: EFCC ta saki surukin Atiku, ta damke lauyansa

Yanzu-yanzu: EFCC ta saki surukin Atiku, ta damke lauyansa

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta saki surukin Atiku, Babalele Abdullahi, kuma akawun manyan kamfanonin da Alhaji Atiku Abubakar ya mallaka.

An damke surukin Atikun ne ranan Asabar amma aka sake shi bayan ta gayyaci lauyansa, Tanimu Turaki, wanda aka damke ranan Litinin.

Kakakin EFCC, Tony Orilade, ya tabbatarwa The Cable cewa an damkesa amma bai bada cikakkun bayanai.

Mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya bayyanawa manema labarai cewa Tanimu Turaki ne babban lauyan da ke shirin kai karan shugaba Buhari kotu kan zaben 2019.

Yace: "Shine shugaban lauyoyin da zasu wakilci Atiku a kotu, kaga daga nan zaka gane dalilin da yasa aka kamashi."

"Shin me yasa shugaba Muhammadu Buhari da APC ke tsoron zuwa kotu? Meyasa suke ta tura mutane iri-iri suna rokon Atiku kar yaje kotu.?"

EFCC a ranar Litinin, 4 ga watan Maris tace tana binciken Alhaji Babalele Abdullahi, daraktan kudi na kamfanonin Atiku Abubakar kan zargin satar kudade.

Abdullahi ya kasance suruki ga Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa da aka kayar a karkashin jam' iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Tony Orilade, mukaddashin kakakin hukumar EFCC, ya fadi hakan a Abuja inda ya tabbatar da cewa Abdullahi na tsare a hannun hukumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel