Akwai bukatar daukar tsaurarran matakiai don ci gaban Najeriya – Babban sakataren gwamnati

Akwai bukatar daukar tsaurarran matakiai don ci gaban Najeriya – Babban sakataren gwamnati

- Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha yace akwai bukatar daukar tsaurarran mataki don ci gaban Najeriya

- Mustapha yace ta hakan ne za a cimma nasara wajen habbaka tattalin arzikin kasar

Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, yace dole a dauki tsaurarran matakai muddin ana son cigaban Najeriya a matsayinta na kasa.

Sakataren ya fadi hakan ne jiya a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Yola, babbar birnin jihar Adamawa.

Akwai bukatar daukar tsaurarran mataki don ci gaban Najeriya – Babban sakataren gwamnati
Akwai bukatar daukar tsaurarran mataki don ci gaban Najeriya – Babban sakataren gwamnati
Asali: UGC

“Zan iya cewa ya zama dole mu dauki tsaurarran matakai ba wanda zai muzanta kowa amma waanda zai bunkasa tattalin arziki da kasar.

“A lokacin da muka karbi mulki a 2015, kimanin jihohi 27 a kasar ba sa iya biyan albashin ma’aikata amma da Shugaban kasar ya shigo lamarin sai ya daidaita, bayan ya dauki tsatsauran mataki."

Akan zaben shugaban kasa da na yan majalissu, Mustapha yace: “Ba tare da cin mutuncin kowa ba, akwai wasu yankuna a kasar nan, a baya, a lokutan zabe, ba a gudanar da zabe kuma duk wanda ya kasance shugaba yana sauka daga shugabanci ko yaki ko yaso.

"Lallai dole muyi aiki don inganta tsarin zabe, ko da yake tsarin bata rasa kurakurai.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu nine dan takarar gwamnan PDP a Kano - Abba Kabir Yusuf

“Muna hira da wani dan Amurka, sai da na tunatar da shi cewa (Micheal) Cohen yana cikin al’umma, yana kuma yunkurin gabatar da shaida, yana kalubalantar zaben Amurka wanda gwamnatin zata kai karshe nan da shekara daya.

“Amma, kawai dai ya kasance jam’iyyar adawa bat a yi bajinta ba kamar yadda ya kamata saboda sun samu kuri’u miliyan 11 ne kacal sabanin miliyan 12 da aka samu a lokacin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayinda mu kuma muka maimaita miliyan 15 kamar yadda muke dashi a baya. Zabbuka na zuwa ne da kalubale amman mungode wa INEC da kokarinta.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel