Mun cafke mutum 323, jami'anmu 2 sun rasa ransu a zaben da ya gabata - Sufeton 'yan sanda

Mun cafke mutum 323, jami'anmu 2 sun rasa ransu a zaben da ya gabata - Sufeton 'yan sanda

- 'Yan sanda sun yi nasarar cafke mutane 323 bisa laifuka daban-daban na zabe

- Jami'an 'yan sanda kwaya biyu ne kacal suka rasa rayukansu a zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 23 ga Fabrairu.

-'Yan sanda za su yi aikinsu babu sani babu sabo a ranar zabe mai zuwa

Hukumar 'yan sandan Nijeriya ta bayyana cewa zuwa yanzu ta cafke mutane akalla guda dari uku da ashirin da uku bisa laifukan zabe daban-daban, a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu.

Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya, Mohammed Adamu ne ya bayyana hakan a jiya Litinin a wani bayani na yadda zabe ya kaya ga manyan jami'an 'yan sanda a Abuja.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: EFCC ta saki surukin Atiku ta damke lauyansa

"Jami'anmu biyu sun rasa rayukansu, inda wasu da dama suka jikkata a lokacin zaben," inji Sufeton."

"Ga duk wani wanda aka kama bisa aikata laifin zabe, na bayar da umarni da a tasa keyarsa zuwa sashenmu na hukunta laifukan zabe don gudanar da cikakken binciki da hadin gwiwar hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, inda daga bisani kuma za mu gurfanar da su don a hukunta su."

Ya kuma kara da cewa, hukumar 'yan sanda na ci gaba da gudanar da shirye-shiryen yin aiki tare da INEC da sauran hukumomin tsaro don tunkarar zabe mai zuwa a ranar 9 ga watan Maris, inda za a zabi gwamnoni da 'yan majalisar dokiki.

"Ina mai kara tabbatarwa da jama'a cewa, hukumar 'yan sanda za ta yi aiki bisa kwarewa wajen ganin an gudanar da sahihin zabe kamar dai yadda aka yi a zaben shugaban kasa.

"Za mu yi amfani da karfin ikon da doka ta sahale mana wajen ganin mun ladabtar da duk wani mutum ko taron mutane da zai yi yunkurin kawo barazana wajen tabbatar da zabe cikin lumana," inji Sufeton 'yan sandan.

Ya kuma gargadi dukkannin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da su kiyaye doka da odar zabe don gudun kawo abubuwan da ka iya jefa kasar nan cikin rikici.

"Rashin kiyaye doka zai jawo wa ko ma wane ne fushin 'yan sanda da ma sauran hukumomin tsaro," Sufeton ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel