'Yan kabilar Ibo sun gabatar da wata babbar bukatar su ga APC kan kujerar Saraki

'Yan kabilar Ibo sun gabatar da wata babbar bukatar su ga APC kan kujerar Saraki

Yayin da harkokin siyasar Najeriya suka soma daukar sabon salo musamman ma ta yadda tuni 'yan siyasa suka fara hankoron siyasar shekarar 2023, tuni dai kasar ta soma daukar harami.

Haka zalika yayin da ake shirye shiryen kaddamar da majalisar tarayya karo na tara tun bayan dawowa mulkin demokradiyya a wannan jamhuriyar, manyan 'yan siyasa daga bangaren al'ummar Ibo sun yi kira ga jam'iyyar APC ta baiwa yankin na su shugaban Sanatoci.

'Yan kabilar Ibo sun gabatar da wata babbar bukatar su ga APC kan kujerar Saraki
'Yan kabilar Ibo sun gabatar da wata babbar bukatar su ga APC kan kujerar Saraki
Asali: UGC

KU KARANTA: EFCC za ta soma bincikar gwamnatin Obasanjo

A cewar su, wannan ne kawai zai sa 'yan kabilar ta Ibo su ji ana damawa da su a harkokin siyasar kasar kuma hakan zai sa 'yan kabilar su dena jin kamar ana nuna masu wariya da tsangwama a tarayyar ta Najeriya.

Tuni dai wasu jiga-jigan 'yan siyasar daga yankin na Inyamurai suka soma dukan gangar bukatar ta su ta kujerar shugaban majalisar dattawa musamman ma ganin cewa shugaban majalisar na yanzu, Dakta Bukola Saraki bai samu nasarar dawowa ba.

A wani labarin kuma, Babban malamin addinin nan na kirisa mai da'awar Annabta watau Udoka Daniel Okechukwu dake zaune a jihar Anambra da yayi hasashen cewa dan takarar shugabancin kasa a PDP, Atiku Abubakar ne zai lashe zaben 2019 ya sake magana.

Fasto Udoka ya bayyana cewa duk da dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta bayyana akasin abun da shi ya hasaso amma dukkan alkaluman sa na cigaba da nuna cewa Atiku din ne dai ya lashe zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel