Yan kwanaki kafin zaben Gwamna: Kansilolin PDP 15 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kwara

Yan kwanaki kafin zaben Gwamna: Kansilolin PDP 15 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kwara

- Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kwara ta sake samun yawan sauyin sheka

- Kansiloli 15 daga kananan hukumomi biyar sun sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Masu sauya shekar sun zargi gwamna mai ci da karya da kuma gaza yin ayyukan komai a jihar

Akalla kansilolin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 15 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar kwara a ranar Litinin, 4 ga watan Maris gabannin zaben Gwamna da na yan majalisar jiha.

Kansilolin wadanda suka kasance daga kananan hukumomi biyar cikin 16 dake jihar, sun bayyana cewa sun koma jam’iyyar APC ne bisa ra’ayin al’umma.

Kamfanin Dillancin Labara Najeriya (NAN) ta rahoto cewa an zabe su ne a karkashin jam’iyyar PDP a watan Nuwamba 2017.

Yayinda yake magana a madadin kansilolin, Hon Suleiman Taoheed mai wakiltan yankin Ajanaku a karamar hukumar Moro, ya bayyana cewa gwamnatin PDP a Kwara ta fadi.

Ya sha alwashin cewa a madadin kansilolin zai hada kan masu zabe a yankunan su don fitowa kwansu da kwarkwatansu domin zabar dukkan yan takara a jam’iyyar APC a ranar Asabar.

Yan kwanaki kafin zaben Gwamna: Kansilolin PDP 15 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kwara
Yan kwanaki kafin zaben Gwamna: Kansilolin PDP 15 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kwara
Asali: UGC

Ya kuma yi alkwarin nuna goyon bayansu ga Abdulrahman Abdulrasak, dan takaran Gwamna a jam’iyyar APC, inda yake bayyana cewa ya tanadi shirye shirye wadanda ke tattare da alkahiri ga jihar.

Ya bayyana cewa za a samu karin kansiloli da zasu dawo APC kafin ranar Asabar.

Yayinda yake karban bakuncin wadanda suka sauya shekar, Dr. Alimi Abdulrasaq, jigon APC kuma dan uwan dan takaran Gwamna ya bayyana cewa ba za su yi nadama ba akan shawarar da suka yanke.

Abdulrasaq ya bayyana cewa idan aka zabi dan uwarsa, zai tabbatar da cewa gwamnatin kananan hukumomi sun samu yancin kansu, sannan zai tabbatar da kusancin gwamnati ga al’umman karkara.

Ya bukace su da su hada kan masu zabe don zaban Abdulrahman Abdulrasaq da dukkan yan takara a karkashin jam’iyyar APC a zaben yan majalisan jiha.

Sunayen wadanda suka sauya shekan sun hada da: Adam Tsado, (Edu), Ogundele Segun, (Isin), James Kayode, (Ilorin ta Gabas), Aremu Jamiu, (Moro), Olorunrinu Suleiman, (Ilorin ta Kudu)

Sauran sun hada da: Omolara Sanni, (Isin), Adebayo Olatayo, (Isin) Saheed Abdulwasiu, (Isin) Saheed Musbau, (Isin) Adeyemi Oladele, (Isin) Suleiman Taoheed, (Isin), Ishola Seunayo, (Isin) da sauran su.

KU KARANTA KUMA: Gwamnati ta tara makudan kudi ta arzikin Ma’adanai a mulkin APC

A wani lamari makamancin haka, mun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Mallam, Nasiru El-Rufa’i ya tarbi tsohon Shugaban NEMA, Alhaji Sani Sidi, wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC tare da magoya bayan sa a jihar Kaduna a ranar Litinin, 4 ga watan Maris.

Sani-Sidi ya bayyana wa gwamnan cewa zasu yi wa jam’iyyar APC aiki don ganin sunyi nasara a zaben da za’ayi a ranar Asabar, 9 ga watan Maris. Ya kara da cewa tun bayan da aka kammala zaben fidda gwani wanda yayi ikirarin ba’a bi zabin mutane ba, babu wani kokari da shugabannin jam’iyyar suka yi don rarrashin wadanda aka muzantawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel