Ana gab da zaben gwamna: El-Rufai ya tarbi mambobin PDP 30,000 a Kaduna

Ana gab da zaben gwamna: El-Rufai ya tarbi mambobin PDP 30,000 a Kaduna

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya tarbi mambobin PDP 30,000 da suka sauya sheka zuwa APC

- Tsohon shugaban hukumar NEMA, Alhaji Sani Sidi ne ya jagoranci masu sauya shekar

- Sidi ya sha alwashin hada kai da APC domin ganin sun cimma nasara a zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar, 9 ga watan Maris

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam, Nasiru El-Rufa’i ya tarbi tsohon Shugaban NEMA, Alhaji Sani Sidi, wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC tare da magoya bayan sa a jihar Kaduna a ranar Litinin, 4 ga watan Maris.

Ku tuna cewa Sani Sidi, wanda ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar PDP ya bayyana sauya shekarsa tare da magoya bayansa 30,000 a ranar Lahadin da ya gabata, shine dan takarar gwamna na biyu da ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Ana gab da zaben gwamna: El-Rufai ya tarbi mambobin PDP 30,000 a Kaduna
Ana gab da zaben gwamna: El-Rufai ya tarbi mambobin PDP 30,000 a Kaduna
Asali: UGC

Sani-Sidi ya bayyana wa gwamnan cewa zasu yi wa jam’iyyar APC aiki don ganin sunyi nasara a zaben da za’ayi a ranar Asabar, 9 ga watan Maris. Ya kara da cewa tun bayan da aka kammala zaben fidda gwani wanda yayi ikirarin ba’a bi zabin mutane ba, babu wani kokari da shugabannin jam’iyyar suka yi don rarrashin wadanda aka muzantawa.

KU KARANTA KUMA: Yaki da rashawa: Jami’an EFCC sun yi ram da tsohon dan takarar shugaban kasa, Turaki

A cewarsa shi da magoya bayan sa a dukkan kananan hukumomi 23 dake fadin jihar sun je gidan gwmnatin ne don su nuna goyan bayan su tare da tabbatar da cewa APC tayi nasara a zaben da za’ayi a karshen makon nan.

“Gwamna El-Rufa’i ya cimma nasarori daban daban a jihar. Sobada haka Ina rokon jama’a su sake zabar shi a zabe mai zuwa,” cewar shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel