Gwamnati ta tara makudan kudi ta arzikin Ma’adanai a mulkin APC

Gwamnati ta tara makudan kudi ta arzikin Ma’adanai a mulkin APC

Wani bincike da jaridar The Cable tayi kwanan nan, ya nuna yadda gwamnatin tarayya ta samu makukun kudi a cikin ‘yan shekarun nan ta hanyar arzikin da Najeriya ta ke da shi a wajen ma’adanai.

Gwamnati ta tara makudan kudi ta arzikin Ma’adanai a mulkin APC
An samu kudin da ba ta taba samun irin su ba a lokacin Fayemi
Asali: UGC

Najeriya dai ta dade ba ta samun wani abin kirki ta harkar hako ma’adanan kasa kafin zuwa gwamnatin nan ba. A 2017 sai da abin da Najeriya ta ke samu da sunan ma’adanai ya tashi da fiye da 500% a karkashin jagorancin Kayode Fayemi.

Hukumar nan ta Nigeria Extractive Industries Transparency Initiative (NEITI) ta fitar da rahoton da ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta samu Dala Biliyan 1.78 ne kacal tun daga 2007 har zuwa shekarar 2016 bayan hawan Buhari mulki.

KU KARANTA: Kotu tace a karbe wasu kudi daga aka sace daga hannun Gwamnati

Wannan rahoto ya kuma nuna cewa a shekarar 2017 kurum, sai da Najeriya ta samu sama da Dala Biliyan 470. Hakan ya yiwu ne bayan da aka nada Kayode Fayemi a matsayin ministan ma’adanai na Najeriya a gwamnatin shugaba Buhari.

Binciken na NEITI wanda aka fitar a Ranar Alhamis ya nuna yadda Najeriya ke samun kudi da arzikin fetur da kuma gas. Tsakanin 2008 zuwa 2009, abin da Najeriya ta ke samu ya fi muni, idan aka auna da abin kasar ta tara tsakanin 2010-2011.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel