An nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki tsakanin PDP da APC game da tsige Sarkin Musulmi

An nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki tsakanin PDP da APC game da tsige Sarkin Musulmi

An shiga cacar baki, nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki tsakanin manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a jahar Sakkwato biyo bayan wasu rade rade dake yawo a farfajiyar siyasar jahar na cewa wata jam’iyya ta dauki alwashin tsige mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar.

Da fari dai jam’iyyar PDP mai mulki a jahar Sakkwato ce ta fara bayyana damuwarta da shirin da ta yi ikirarin jam’iyyar APC ta kulla na cewa idan har ta samu nasara a zaben gwamnan jahar da zai gudana a ranar 9 ga watan Maris, lallai za ta tsige Sarkin Musulmi, ta nada sabo.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Jami’an EFCC sun yi ram da tsohon dan takarar shugaban kasa, Turaki

An nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki tsakanin PDP da APC game da tsige Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi
Asali: UGC

A ranar Litinin, 5 ga watan Maris ne wasu matasa suka shirya tattaki a cikin garin Sakkwato har zuwa fadar mai alfarma sarkin Musulmi, inda suka bayyana makasudin shirya gangamin shine don ankarar da Sarkin game da shirin da APC ke yin a tsigeshi daga kujerarsa.

Shugaban matasan, Murtala Abdulrahman ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa “Mun zo fadar Sarkin Musulmi ne don sanar dashi game da mugun shirin da APC ke yin a tsigeshi daga kujerarsa idan har ta samu nasara a zaben gwamna mai zuwa.

“Saboda APC tana zargin Sarki baya goyon bayanta, don haka suke kirarin ‘Sabon gwamna, sabon Sarki’, mu kuma ba zamu zuba idanu suna cin mutuncin shuwagabannin ba, sai mun basu kunya.” Inji shi.

Sai dai jam’iyyar APC ta musanta wannan zargi na jam’iyyar PDP, sa’annan ta yi tir da gangamin da matasan suka shirya, inda ta bayyanasu a matsayin Sojojin haya da ake daukan nauyinsu don su bata ma jam’iyyar suna.

Shugaban APC reshen jahar Sakkwato, Isa Acida ne ya musanta zargin da PDP ke yi ma jam’iyyar APC, inda yace shugaban PDP, Ibrahim Milgoma ne ya fara yayata wannan jita jita da nufin jefa jahar Sakkwato cikin rikici.

A cewar Acida, Milgoma tare da shugaban PDP na yankin Arewa maso yamma, Muhammadu Dangwaggo da kuma sauran shuwagabannin jam’iyyar ne suka fara watsa wannan labarin karya a yayin gangamin yakin neman zabe da suka shirya a ranar Asabar a fadar gwamnatin jahar Sakkwato.

Don haka yayi kira ga hukumomin tsaro dasu dauki matakin kare jama’an jahar Sakkwato, saboda manufar jam’iyyar PDP shine jefa jahar cikin tashin hankali yayin da zaben gwamnoni ke karatowa don kada zaben ya tabbata a jahar Sakkwato.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel