An bankado shirin wasu yan siyasa na danganta Ganduje da wani mummunan abin kunya

An bankado shirin wasu yan siyasa na danganta Ganduje da wani mummunan abin kunya

Zuwa yanzu dai ta bayyana siyasar Kano na cigaba da daukar zafi wanda hakan yasa bangarori masu hamayya da juna na ta kirkirar hanyoyin da zasu goga ma dayan bangaren kashin kaza don hakan ya basu damar tallata kansu, da nufin samun nasara.

Sai dai wani sabon salo da abokan hamayyar gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, suka bullo dashi, musamman matasan Kwankwasiyya ke watsa shi a shafukan sadarwar zamani, ya kasance na batanci mai muni.

KU KARANTA: Doguwa ya bayyana dalilin da yasa jigogin PDP a Kano suka raba jaha da Kwankwaso

Legit.ng ta kasance ganau ne ba jiyau yadda wasu ma’abota kafafen sadarwar zamani dake hamayya da gwamnatin jahar Kano suke watsa wasu hotuna wani babban mutumi babu wando a jikinsa, inda suke danganta hoton ga Gwamna Ganduje da sunan yana lalata da wata.

Sai dai bincikenmu ya tabbatar da wadannan hotunan ba gaskiya bane, hotunan karya ne ake dangantasu da gwamnan, amma maganan gaskiya shine hotunan wani Sanata ne da aka taba dauka a shekarun baya yayin da yake tare da wata farkarsa, kuma jaridar Sahara Reporters ce ta fara wallafa hotunan.

A wancan lokaci da rahoton Sanatan ya bayyana, bama hotuna kadai ba, hatta bidiyon lamarin ya watsu a shafukan sadarwa inda muryar Sanatan dake cikin bidiyon tare da na budurwa data dauki hoton suka bayyana karara.

Hatta da aka tambayi Sanatan da abin ya shafa ko menene gaskiya wadannan hotuna da kuma bidiyon sai ya kada baki yace “Ai wannan rayuwata ce.”, ma’ana baya bukatar yi ma wani bayanin abinda ya aikata saboda rayuwarsa yake yi.

Da wannan ake jan hankalin jama’a dasu ankara da cewa wadannan hotuna ba hotunan gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje bane, domin masu yayata hotunan na barazanar sakin cikakken hoton don bata ma gwamnan suna.

A wani labarin kuma, hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta bayyana cewa har yanzu Abba Kabir Yusuf inkiya Abba gida gida ta sani a matsayin dan takarar gwamnan jahar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar PDP saboda babu wanda ya mika mata hukuncin da wata kotu ta yanke dake haramta takarar Abba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel