Ban da niyyar hana Gwamna Abiola Ajimobi bin Tawagar APC – Tinubu

Ban da niyyar hana Gwamna Abiola Ajimobi bin Tawagar APC – Tinubu

A jiya Litinin ne babban jigon APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya maida martani game da rade-radin da ake yi na cewa ya haramtawa gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi yi wa jam’iyyar APC kamfe.

Ban da niyyar hana Gwamna Abiola Ajimobi bin Tawagar APC – Tinubu
Tinubu yace Gwamna mai shirin barin mulki Ajimobi yana da amfani a APC
Asali: Depositphotos

Asiwaju Bola Tinubu ya karyata cewa akwai wata rigima tsakanin sa da gwamna mai-ci Abiola Ajimobi na Oyo. Tsohon gwamnan na jihar Legas yace Abiola Ajimobi, babban abokin tafiyar sa ne a jam'iyyar APC ba wai abokin hamayyar sa ba.

Bola Tinubu yayi maza ya karyata labarin da ake ta faman yada na cewa yana sa-in-sa da gwamnan na jihar Oyo mai shirin barin gado, a kokarin janyo Cif Adebayo Alao-Akala cikin APC daf da zaben gwamnoni da za ayi kwanan nan.

Jagoran na APC yake cewa gwamna Abiola Ajimoni yana cikin wadanda su ke ji da su a jam’iyyar APC saboda irin jajircewar da yayi tsayin-daka a tafiyar su, da kuma irin ayyuka na a-zo-a-gani da yayi wa jihar sa ta Oyo a kan karagar mulki.

KU KARANTA: Tinubu ya dakatar da gwamnan Oyo daga halartar kamfen a jihar sa

Tinubu duk ya bayyana wannan ne ta bakin wani babban Hadimin sa mai suna Tunde Rahman, wanda yake magana a madadin sa. Mista Rahman yayin kaca-kaca da jaridar Sahara Reporters inda yace labaran su duk ba gaskiya bane.

Tsohon gwamnan na jihar Legas yake cewa wadanda su ke wannan jita-jita, wasu ne a gefe da ke bakin ciki da nasarar da APC ta samu a zaben shugaban kasa. Tinubu yace sam bai da niyyar hana gwamna mai-iko shiga cikin kamfe a APC.

Bayan cewa bai da karfin ikon da zai haramtawa gwamnan APC shiga cikin jirgin yakin neman zabe, babban jagoran na jam’iyyar mai mulki a kasar ya bayyana cewa babu yadda za ayi, ya iya hana gwamna zuwa wani taro a cikin jihar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel