Wadanda su kayi takara da Atiku sun ba sa shawara ya rabu da zuwa Kotu

Wadanda su kayi takara da Atiku sun ba sa shawara ya rabu da zuwa Kotu

– Wasu ‘Yan takara da su ka nemi shugaban kasa sun taya Buhari murnar lashe zabe

– ‘Yan takarar har su 12 sun yi kira ga Atiku da ya ajiye maganar zuwa gaban Alkalai

– Wadanda su ka nemi mulkin sun ba Atiku shawara ya hakura ya taya Buhari murna

Wadanda su kayi takara da Atiku sun ba sa shawara ya rabu da shiga Kotu
An ba Atiku shawara ya janye batun zuwa Kotu da Buhari
Asali: Twitter

Wasu ‘yan takara har su 12 da su ka nemi mulkin Najeriya a zaben 2019, sun taya Buhari murnar nasarar da ya samu a zaben 23 na Watan Fubrairu. Masu neman mulkin sun kuma yi kira na musamman ga Alhaji Atiku Abubakar.

‘Yan takarar da ke karkashin lemar “Forum of Presidential Candidates and Political Parties for Good Governance” a Najeriya sun ce ba su da matsala da nasarar da shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaben na bana da aka yi.

Shugaban wannan tafiya, Shittu Kabir, yayi kira ga Atiku Abubakar wanda ya zo na biyu a zaben da cewa ya ajiye makaman yakin sa, ya hakura da batun shiga kotu. Kabir yace dole dai mutum daya ne zai yi nasara a wannan zabe.

KU KARANTA: Wani Lauya ya ba Atiku Abubakar shawara ya hakura da zuwa Kotu

Shittu Kabir na jam’iyyar APDA yayi wannan kira ne lokacin da ya gana da manema labarai a madadin sauran ‘yan takarar na 2019. Kabir yace bai kamata Atiku na PDP ya biyewa masu ba sa shawarar ya ruga kotu ya kai kara ba.

‘Dan takarar yace shugaba Muhammadu Buhari da Alhaji Abubakar, kamar ‘yan uwan juna su ke, don haka yake ganin gara Atiku rungumi kaddara a hakura cewa jama’a sun zabi APC ta cigaba da mulki, duba da irin tarin shekarun sa.

Sauran ‘yan takarar su ne; Edozie Madu, Danjuma Mohammed, Mamman Naptali, da kuma Ahmed Buhari wanda dama tuni su ka nuna cewa su na goyon bayan tazarzen shugaban kasa Buhari na APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel