An ba EFCC dama ta karbe wasu kudi sama da Miliyan 700 ta ba Gwamnati

An ba EFCC dama ta karbe wasu kudi sama da Miliyan 700 ta ba Gwamnati

Babban Alkali mai shari’a na kotun tarayya da ke Abuja, ya bada dama ga hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta karbe wasu makudan kudi ta mikawa gwamnati.

An ba EFCC dama ta karbe wasu kudi sama da Miliyan 700 ta ba Gwamnati
Miliyan 700 da aka sace daga PAP za su shiga asusun Gwamnatin Buhari
Asali: UGC

Alkali James Tsoho ya ba hukumar EFCC damar karbe kudi har Naira Miliyan 732.85, da kuma wani katafaren fili da ke kan hanyar Katsina Road a karamar hukumar Kaduna ta Arewa da ke jihar Kaduna da aka mallaka ta haram.

Wannan fili kurum ya haura Naita miliyan 190 idan aka jefa sa a kasuwa kamar yadda wani mukaddashin kakakin hukumar EFCC din watau Tony Orilade ya bayyana. Yanzu wannan dukiya ta dawo cikin lalitar Najeriya.

KU KARANTA: Lauyan da ya taso Ganduje a gaba yana shirin maka Magu a Kotu

Hukumar EFCC tana zargin cewa an mallaki wadannan dukiyoyi ne ta hanyoyin da ba su dace ba, don haka ta garzaya kotu tana mai nema a bata dama ta karbe wannan tarin kudi su dawo zuwa cikin asusun gwamnatin tarayya.

A baya dai kotu ta nemi a maidawa gwamnatin kudin kafin a karasa bincike. Yanzu kuwa an bada hukuncin cewa komai ya dawo cikin asusun gwamnatin tarayya. Sauran wanda EFCC ke kara sun hada da Martins Olajide da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel