Buhari ya karbi bakuncin mambobin kwamitin kamfen din sa, hoto

Buhari ya karbi bakuncin mambobin kwamitin kamfen din sa, hoto

A daren yau, Litinin, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin mambobin kwamitin yakin neman zaben sa (PCC) a fadar sa, Villa da ke Abuja.

Shugaba Buhari ya shirya wa mambobin PCC liyafa ne domin nuna jin dadin sag a irin aikin da su ka yi, wanda ya kai ga jam’iyyar APC ta lashe zaben kujerar shugaban kasa.

Liyafar da aka fara da misalign karfe 8:10 na dare ta samu halartar shugaban kwamitin kamfen din Buhari, Rotimi Amaechi, tsohon shugaban majalisar dattijai, Ken Nnamani, Sanata Ali Ndume, Sanata Abdullahi Adamu, da tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu.

Ragowar su ne sakataren gwanatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ministan ilimi, Adamu Adamu, da sauran su.

Buhari ya karbi bakuncin mambobin kwamitin kamfen din sa, hoto
Buhari ya karbi bakuncin mambobin kwamitin kamfen din sa, hoto
Asali: Twitter

Jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, da ake sa ran zai gabatar jawabi, bai halarci taron ba har ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto.

DUBA WANNAN: Magudin zabe: Za mu karbi kujerun mu daga hannun PDP – Buhari

Kazalika, shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, da shi ma zai gabatar da jawabi bai halarci wurin liyafar ba.

A watan janairu ne shugaba Buhari ya kaddamar da PCC da sunan sa a matsayin shugaba da na Tinubu a matsayin shugaba na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel