Magudin zabe: Za mu karbi kujerun mu daga hannun PDP – Buhari

Magudin zabe: Za mu karbi kujerun mu daga hannun PDP – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa jama’ar jihar Akwa Ibom tabbacin cewar za su karbi dukkan kujerun ‘yan takarar sun a majalisar tarayya da PDP ta kwace ta hanyar tafka magudi a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

Buhari ya fadi hakan ne ta bakin mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya wakilce shi a wani taron gana wa da jama’ar jihar domin yi ma su godiyar kuri’un da su ka kada wa jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa.

Ya bayyana cewar abu ne marar yiwuwa a ce tsohon gwamnan jihar, Sanata Godswill Akpabio, ya fadi takarar kujerar sanata a zaben da aka yi.

Fashi ne aka yi wa jam’iyyar APC a ranar 23 ga watan Fabrairu. An sace kuri’un jama’a, an canja sakamakon zabe amma duk da haka ba za m karaya ba. Za mu tabbar da cewar mun karbo dukkan hakkin mu da aka kwace ma na ranar 23 ga wata.

Magudin zabe: Za mu karbi kujerun mu daga hannun PDP – Buhari
Buhari da Osinbajo
Asali: UGC

“Abu ne da ba zai yiwu ba a ce Akpabio ya fadi zabe. Ba mu da shakku a kan cewar shine ya lashe zabe amma INEC ta yi ma sa kwace,” a kalam Osinbajo.

DUBA WANNAN: Zabe: Kotu ta kori karar da PDP ta shigar da gwamnan APC

Mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga jama’a da su yi tururuwa domin fita su kada wa jam’iyyar APC kuri’a a zaben gwamnoni da na mambobin majalisar dokoki.

Da ya ke gabatar da na sa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya ce sun ziyarci jihar ne domin godiya ga jama’a ba wai don jajen abinda ya faru a baya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel