SERAP ta maka gwamnatin Najeriya gaban Kuliya kan muzgunawa 'yan jarida

SERAP ta maka gwamnatin Najeriya gaban Kuliya kan muzgunawa 'yan jarida

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta SERAP, ta maka gwamnatocin Najeriya har gaban babbar kotun kungiyar kasashen Afirka ta Yamma da ke garin Abuja bisa zargin muzgunawa 'yan jarida da kuma manema labarai a kan bakin ayyukan su.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa, kungiyar kare hakkin bil Adama ta SERAP, ta maka gwamnatin tarayya da kuma ta jihohin Najeriya a gaban babbar Kotun ECOWAS kan laifi na cin zarafi, barazana gami da rashin adalci ta fuskar muzgunawa 'yan jarida da kuma manema labarai.

SERAP ta maka gwamnatin Najeriya gaban Kuliya kan muzgunawa 'yan jarida
SERAP ta maka gwamnatin Najeriya gaban Kuliya kan muzgunawa 'yan jarida
Asali: Twitter

Kungiyar SERAP ta shigar da koken ta gaban babbar Kotun dangane da yadda gwamnatocin Najeriya ke ribatar karfin iko wajen cin zarafi da muzgunawa manema labarai yayin da suka watsa rahotanni masu cin karo ko kuma sukar akidu da tsare-tsaren su.

Cikin korafin ta mai lamba ECW/CCJ/APP/09/19 da ta shigar a gaban Kotun ta ECOWAS, kungiyar SERAP ta bayyana rashin jin dadin ta dangane da yadda gwamnatocin Najeriya ke dakilewa manema labarai 'yancin su da kuma masu amfani da zaurukan sada zumunta wajen bayyana ra'ayoyin su.

KARANTA KUMA: Wani Matashi ya shiga hannu da laifin kisan Mahaifiyar sa a Filato

Kungiyar SERAP da sanadin babban Lauya mai kare hakkin dan Adam, Mista Femi Falana, ta nemi kotun da ta ƙayyade hurumi ko kuma iko na gwamnatocin Najeriya wajen haramtawa manema labarai yada rahotanni bisa ga madogara da kuma tanadi na 'yancin su.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, babbar kungiyar mai fafutikar kare hakkin bil Adama ta shigar da korafin ta domin neman kotu ta tsawatar tare da sanyawa gwamnatocin Najeriya iyaka ta sakarwa manema labarai marar su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel