Zaben Gwamnoni: Jihar Legas ta bayyana ranar Juma’a a matsayin hutu ga makarantu

Zaben Gwamnoni: Jihar Legas ta bayyana ranar Juma’a a matsayin hutu ga makarantu

Gwamnatin jihar Legas ta bada umurnin cewa a sake baiwa makarantu hutu a ranar Juma’a, 8 ga watan Maris, 2019.

A cewar bayanai daga ma’aikatar ilimi, dukkan makarantun gwamnati da makarantu masu zaman kansu a jihar za su rufe a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris,2019, sannan su dawo a ranar Litinin, 11 ga watan Maris, 2019.

Jawabin ya bayyana cewa wannan ya zama dole ne don gyara sabani da aka samu na cewa makarantu ba za su bude ba a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris.

Zaben Gwamnoni: Jihar Legas ta bayyana ranar Juma’a a matsayin hutu ga makarantu
Zaben Gwamnoni: Jihar Legas ta bayyana ranar Juma’a a matsayin hutu ga makarantu
Asali: Facebook

Jawabin ya cigaba da bayyanawa cewa hutun zai tabbatar da cewa dukkan dalibai sun kasance a gidajen su a lokacin gudanar da zaben gwamnoni da majalisar jihohi wanda za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Babu ja da baya wajen kai kara kotu kan zaben Shugaban kasa na 2019 - PDP

Jawabin har ila yau, ya bukaci dukkan iyaye, malamai da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da al’umma gaba daya da su zauna a gida a wannan lokacin.

A wani lamari na daban, mun ji cewa yau, Litinin, 4 ga wata, ne wata kotun gwamnatin tarayya da ke jihar Neja ta kori wata kara da jam’iyyar PDP ta shigar da gwamnan jihar, Abubakar Bello, a kan zargin sa da amfani da karatu na bogi.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewar jam’iyyar PDP ta shigar da karar gwaman domin neman ta soke takarar sa bisa zargin cewar ya gabatar da takardun karatu na bogi a cikin kunshin takardun da ya mika wa hukumar zabe ta kasa (INEC).

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel