Zabe: Kotu ta kori karar da PDP ta shigar da gwamnan APC

Zabe: Kotu ta kori karar da PDP ta shigar da gwamnan APC

- Wata kotun gwamnatin tarayya da ke jiar Neja ta tabbatar wa da gwamnan jihar, Abubakar Bello, takarar sa a zaben gwamnoni da za a yi

- Jam’iyyar PDP ce ta shigar da karar gwamnan bisa zargin sa da gabatar da takardun karatu na bogi

- Kotun ta yi watsi da karar ne bisa dogaro da rashin gabatar da kwakwarar hujja da shaidar jam’iyyar PDP ya yi a gaban kotun

A yau, Litinin, 4 ga wata, ne wata kotun gwamnatin tarayya da ke jihar Neja ta kori wata kara da jam’iyyar PDP ta shigar da gwamnan jihar, Abubakar Bello, a kan zargin sa da amfani da karatu na bogi.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewar jam’iyyar PDP ta shigar da karar gwaman domin neman ta soke takarar sa bisa zargin cewar ya gabatar da takardun karatu na bogi a cikin kunshin takardun da ya mika wa hukumar zabe ta kasa (INEC).

Zabe: Kotu ta kori karar da PDP ta shigar da gwamnan APC
Abubakar Sani Bello
Asali: UGC

Sai dai, alkalin kotun, Jastis Aminu Aliyu, ya bayyana cewar shigar da karar bayan wucewar wa’adin kwanaki 14, ya saba da sashe na 285 (9) na kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 1999.

DUBA WANNAN: Boko Haram: ISWAP ta tsige Albarnawi, ta nada sabon shugaba

Sannan ya kara da cewa shaidan da jam’iyyar PDP ta gabatar ya gaza gamsar da kotu yayin amsa tambayoyin da aka yi ma sa a kan cewar gwaman ya gabatar da takardun karya ga INEC.

A saboda haka ne kotun ta bayyana cewar babu hurumin cigaba da sauraron karar, sannan ta bukaci a biya wadanda aka yi kara N500,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel