Babu ja da baya wajen kai kara kotu kan zaben Shugaban kasa na 2019 - PDP

Babu ja da baya wajen kai kara kotu kan zaben Shugaban kasa na 2019 - PDP

Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Litinin, 14 ga watan Maris sun bayyana cewa sun yanke shawarar tunkarar kotun karar zabe akan sakamakon zaben Shugaban kasa wanda ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Iyayen jam’iyyar sunce ba za su rusa shirin PDP da dan takararta, Atikun Abubakar ba dake neman daukar matakin doka akan zaben.

Da yake magana, a wani taron manema labarai a Abuja bayan ganawar masu ruwa da tsaki, babban sakataren jam’iyyar na kasa, Kola Ologbodiyan yae iyayen jam’iyyar sun yanke shawarar cewa ba za ta ji tsoron kowace barazana daga jam’iyya mai mulki ba ko kuma amfani da karfi wajen hana dan takararta Atiku Abubakar neman hakkinsa ba akan sakamakon zaben kasar.

Babu ja da baya wajen kai kara kotu kan zaben Shugaban kasa na 2019 - PDP
Babu ja da baya wajen kai kara kotu kan zaben Shugaban kasa na 2019 - PDP
Asali: Facebook

Ologbodiyan yace yayinda PDP ta yaba ma yan Najeriya kan kin aminewa da tursasa masu sojoji da jam’iyya mai mulki tayi, jam’iyyar ta yanke shawarar neman hakkinta a kotun zabe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: EFCC na binciken surukin Atiku kan zargin satar kudade

Ya kuma ce uwar jam’iyya ta sake duba halin da ake iki a Kano musamman yayinda kotu ta yanke hukuni sannan kuma cewa an tura roko akan hukuncin.

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa tana sane da biyan wasu jam’iyyu da AP tayi domin su hana Atiku shiga kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel