Karyane, Buhari bai cire gwamnan CBN ba

Karyane, Buhari bai cire gwamnan CBN ba

Babban bankin Najeriya CBN ta karyata rahotannanin da ke yawo cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sallami gwamnan bankin, Godwin Emefiele.

Bada amsa kan wannan tambaya, diraktan yada labarai bankin, Mista Isaac Okorafor, ya bayyanawa manema labarai cewa gwamnan bankin na ofishinsa yana aiki yanzu, saboda haka babu gaskiya cikin al'amarin.

Kana wani ma'aikacin bankin ya bayyanawa jaridar The Nation cewa gaskiya babu gaskiya cikin jita-jitan, gwamnan yana aiki kuma wa'adinsa zai kare a wata Yuni.

Yace: "Bugu da kari, yanada bukukuwan da zai halarta gobe, wanda shine ganawa da masu ruwa da tsaki kan arzikin auduga a ranan Talata, 5 ga watan Maris, 2019."

Majiya daga fadar shugaban kasa ya bayyanawa The Cable cewa karyane.

Yace: " Shugban kasa bai da ikon cire gwamnan CBN ba tare da amincewar majalisar dattawa ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel