Wani Matashi ya shiga hannu da laifin kisan Mahaifiyar sa a Filato

Wani Matashi ya shiga hannu da laifin kisan Mahaifiyar sa a Filato

Wata babbar Kotu da ke zaman ta a birnin Jos na jihar Filato, ta zartar da mafi muni hukunci na kisan kai ta hanyar rataya kan wani Matashi mai shekaru 20 a duniya, Agugu Adau, bisa laifin da ya aikata na kisan Mahaifiyar sa.

Alkaliyar Kotun, Mai shari'a Nafisa Musa, ita ta zartar da wannan babban hukunci bayan kama Matashi Adau dumu-dumu da laifin sa na sanadiyar kawo karshen numfashin Mahaifiyar sa a ban kasa kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Bisa ga dalilai na shaidu gami da kwararan hujjoji da aka gabatar, babbar Kotun ba bu ko tantama ta cafke Matashin da laifin mugunyar ta'ada ta kisan Mahaifiyar sa ba tare da tausayi ko jin kanta ba.

Wani Matashi ya shiga hannu da laifin kisan Mahaifiyar sa a Filato
Wani Matashi ya shiga hannu da laifin kisan Mahaifiyar sa a Filato
Asali: Twitter

Shafin jaridar The Nation ya ruwaito cewa, Matashi Adau ya aikata wannan mummunar ta'ada a ranar 30 ga watan Dasumba na shekarar 2016 da ta gabata bayan da Mahaifiyar sa ta hau kujerar naki wajen ba shi gadon wata Layar Zana da Mahaifin sa ya Mutu ya bari.

KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga sun kashe Sojoji 3 a jihar Ribas

Rahotanni sun bayyana cewa, Agugu bayan sheke Mahaifiyar sa har Lahira a kauyen Kisaghyip da ke karkashin karamar hukumar Bassa ta jihar Filato, ya kuma yiwa awon gaba da kudin ta kimanin N20,000 inda ya ci karen sa ba bu babbaka wajen sayen ababen more rayuwa.

Matashi Agugu yayin amsa laifin sa a gaban Kuliya ya kuma bayyana cewa, ya yanke hukuncin kashe Mahaifiyar sa bayan da ya yi daraf akan dokin zuciya a sakamakon hana shi gadon wata Layar zana da Mahaifin sa malamin tsubbu ya Mutu ya bari a gidan Duniya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel