Yanzu Yanzu: Kotu ta kori karar da aka shigar akan gwamnan jihar Adamawa

Yanzu Yanzu: Kotu ta kori karar da aka shigar akan gwamnan jihar Adamawa

Babban kotun Babban Birnin Tarayya a Apo, a ranar Litinin ta kore karar dake zargin gwamna Mohammed Bindow na Adamawa da gabatar da takardun kammala makaranta na bogi ga hukumar zabe ma zaman kanta (INEC) akan rashin iko.

Yayinda yake gabatar da hukunci, Justis Olukayode Adeniyi, ya riki kotun da rashin ikon sauraran karan bisa dalilin cewa karar ta zo ne daga jihar Adamawa inda ya kamata a daukaka ta ba a babbar birnin tarayya ba.

Wata kungiya mai zaman kanta, a karkashin kungiyar Incorporated Trustees of Kingdom Human Rights Foundation International, ta gabatar da kara kotun inda take zargin gwamnan da mallakar takardun bogi

An zargi gwamnan da gabatar da takardun bogi ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC, inda yake nunin cewa ya rubuta jarabawar WAEC a watan Yuni, 1983.

Kungiyan ta fada wa kotun cewa sabanin ikirarin karya da mai laifin yayi cewa yayi makarantar Government Secondary School, Miango Dake jihar Filato, “tabbatattun shaidu sun nuna cewa Gwamna Bindow bai taba halartan makarantan ba balle zaman jarrabawar WAEC da zai bashi daman karban takardun shaida”.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: EFCC na binciken surukin Atiku kan zargin satar kudade

Mai karan na neman a soke takarar Bindow akan rashin cancantarsa da takaran gwamna a zaben 2019.

Bindow a nashi jawabin, ya musanta zargin gabatar da takardun bogi ga INEC kamar yanda ake ikirari.

Gwamnan ta hannun lauyan sa, Cis Chris Uche, SAN, ya fada wa kotun cewa ya lashe zaben fidda gwani da jam’iyyar APC ta gudanar a watar Oktoba 2018 a Yola.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel