Yanzu-yanzu: An hallaka mutane 40 a jihar Zamfara

Yanzu-yanzu: An hallaka mutane 40 a jihar Zamfara

Wasu yan bindiga sun kai mumunan farmaki kananan hukumomin Shinkafi da Anka a jihar Zamfara inda suka hallaka akalla mutane 40. Yan bindigan sun shiga cikin garin kan babura.

Kakakin atisayen Opration Sharar Daji ya tabbatar da wannan rahoton ga manema labarai amma yace daga baya zasu saki yawan wadanda suka rasa rayukansu.

Game da cewarsa, kwamandan ayyuka ya isa kananan hukumomin domin ganin abinda ya faru da kuma bayar da tsaro.

Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu, ya gaza tabbatar da labarin da kuma yawan mutanen da aka kashe.

A ranan Alhamis da ya gabata, akalla mutane 30 suka rasa rayukansu a garin Kware, kusa da karamar hukumar Shinkafi.

KU KARANTA: Da kamar wuya - Babban lauyan Femi Falana

Mazaunan garin sun bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun shigo sun harbin kan mai uwa da wabi kuma suka bankawa gidaje da shaguna wuta.

Wani mazauni mai suna Musa Dan Doki yace: "Sun zagaye garin sannan suka fara bankawa gidaje wuta. Duk wanda ya fito daga gidanje sai su harbeshi. An birne mutane 30 zuwa yanzu, muna cikin mawuyacin fitina."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel