Dankari: Jam'iyyu 49, yan takara 32, sun janyewa Nasir El Rufa'i a takarar gwamnan jihar Kaduna

Dankari: Jam'iyyu 49, yan takara 32, sun janyewa Nasir El Rufa'i a takarar gwamnan jihar Kaduna

Akallayan takaran gwamnan jihar Kaduna 32 sun hada kai wajen janyewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El Rufa'i na jam'iyyar APC a zaben da za'a gudanar ranan 9 ga watan Maris, 2019.

Sun yanke wannan shawara ne ranan Litinin, inda yan takara 32 daga jam'iyyu 49 suka amince da shu a matsayin dan takara daya tilo da suka yarda da shi.

Shugaban jam'iyyar United Democratic Party (UDP), Comrade Auwal Abdullahi Aliyu, ya ce sun fito fili domin marawa gwaman baya ne domin taimaka masa wajen cigaba da ayyukan kwarai da ya fara kuma ya cancanci haka.

Game da cewarsa: "Mun dade muna tattaunawa kuma mun yanke shawaran cewa saboda soyayyar jihar Kaduna. Mun san cewa ba zamu ci wannan zabe ba, abinda mukayi niyyar yi shi ya fara, saboda haka mun yanke goya masa baya."

"Ba kawunanmu muke kallo ba, jihar Kaduna da mutanenta muke kallo."

Yace duk da cewan sunada nasu shirye-shiryen, suna goyon bayansa domin ceto jihar Kaduna.

Auwal Aliyu UDP, Matoh Yakubu AGA, Umar Uba NIP, Fatima Uba RP, Kabiru Idris MPN, Ahmed Zagi GPN, Mansur Suleiman AA, Alhaji Yahaya Marafa UPN, Abdulfatai Yusuf WTPN and Umar Suleiman Abubakar DA, Jubril Muhammed ID

Yan takaran da suka janye masa sune: Auwal Aliyu UDP, Matoh Yakubu AGA, Umar Uba NIP, Fatima Uba RP, Kabiru Idris MPN, Ahmed Zagi GPN, Mansur Suleiman AA, Alhaji Yahaya Marafa UPN, Abdulfatai Yusuf WTPN and Umar Suleiman Abubakar DA, Jubril Muhammed ID

Sauran sune; Mustapha Bakano APA, Haliru Tafida MRDD, Abubakar Aliyu CAP, Abubakar Abdullahi ZLP, Aminu Sabo ANNP, Hajiya Rabiatu Suleiman Shula NAC, Kabiru Jibril PPA, Adamu Idris Chado DPC, Suleiman Abdulrasheed MMN, Sani Abdulkadir, Mohammed Jamilu Accord Party and Yahaya Solomon NPC da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel