Yanzu Yanzu: EFCC na binciken surukin Atiku kan zargin satar kudade

Yanzu Yanzu: EFCC na binciken surukin Atiku kan zargin satar kudade

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) a ranar Litinin, 4 ga watan Maris tace tana binciken Alhaji Babalele Abdullahi, daraktan kudi na kamfanonin Atiku Abubakar kan zargin satar kudade.

Abdullahi ya kasance suruki ga Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa da aka kayar a karkashin jam' iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Tony Orilade, mukaddashin kakakin hukumar EFCC, ya fadi hakan a Abuja inda ya tabbatar da cewa Abdullahi na tsare a hannun hukumar.

Yanzu Yanzu: EFCC na binciken surukin Atiku kan zargin satar kudade
Yanzu Yanzu: EFCC na binciken surukin Atiku kan zargin satar kudade
Asali: Twitter

"Muna bincikar Abadullahi akan wani lamari da ya shafi zambar kudi.

"Za mu yi magana a lokacin da ya kamata," cewar Orilade kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Rahoton yace ba a bashi damar bayyana adadin kudin da ake zargin Abdullahi da sacewa ba. Sai dai NAN tace bincike ya nuna cewa kudin ya kai kimanin kudin ingila wato Euro miliyan 150.

KU KARANTA KUMA: Hukumar INEC tayi magana akan zargin sace takardun sakamako a Zamfara

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Atiku Abubakar ya sake yin magana biyo bayan kama surukinsa, Babalele Abdullahi da lauyansa cewa suna biyan bashin mara masa baya da suka yi ne.

Atiku ya fadi zaben Shugaban kasa inda Muhammadu Buhari yayi nasara koda dai dan takarar na jam’ iyyar Peoples Democratic Party ya ki amincewa da sakamakon zaben sannan ya sha alwashin zuwa kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel