‘Yan sanda sun kubutar da alkalin alkalan jihar Nasarawa da ‘yan JUSUN su ka garkame

‘Yan sanda sun kubutar da alkalin alkalan jihar Nasarawa da ‘yan JUSUN su ka garkame

Da yammacin yau, Litinin, ne rundunar ‘yan sanda reshen jihar Nasarawa su ka bayyana cewar sun kubutar da Jastis Suleiman Umar, alkalin alkalan jihar da mambobin kungiyar ma’aikatan shari’a (JUSUN) su ka garkame a ofishin sa.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Ordiah, ne ya sanar da hakan a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar. Mataimakin kwamishinan ya raka Jastis Umar ya bar ofishin sa bayan an kubutar da shi.

Da safiyar yau ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa mambobin kungiyar ma'aikatan sharia karkashin inuwar kungiyar JUSUN reshen jihar Nasarawa, sun garkame babban alkali na jihar Nasarawa, mai shari'a Suleiman Umar Dikko a cikin ofishinsa.

‘Yan sanda sun kubutar da alkalin alkalan jihar Nasarawa da ‘yan JUSUN su ka garkame
‘Yan sanda sun kubutar da alkalin alkalan jihar Nasarawa da ‘yan JUSUN su ka garkame
Asali: Twitter

JUSUN na ikirarin cewa babban alkalin jihar na rage wani kaso daga cikin albashin kowanne ma'aikaci a shekara.

Idan za a iya tunawa, kungiyar JUSUN ta shiga yajin aiki tun a ranar 13 ga watan Nuwamba, 2018.

DUBA WANNAN: Da hannun wasu mayan a rashin zaman lafiyar jihae Benuwe - Rundunar soji

Shugaban JUSUN na jihar Nasarawa, Kwamred Jimoh Musa, ya ce kungiyar ta samu hadin kan uwar kungiya ta kasa da shugabancin jihohi 18 na kasar nan.

Gwamnatin jiha na biyan mu albashi amma tsawon wata hudu kenan alakalin alakai ya ki biyan mu saboda mun shiga yajin aiki,” a cewar Musa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel