'Yan Bindiga sun kashe Sojoji 3 a jihar Ribas

'Yan Bindiga sun kashe Sojoji 3 a jihar Ribas

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, wasu 'yan bindiga dadi sun hallaka sojoji uku cikin yankin Obonoma da ke karkashin karamar hukumar Akuku-Toru ta jihar Ribas a ranar Asabar ta makon da ya gabata.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, sanye cikin tufafi na Dakarun soji, 'yan bindiga sun kai hari sansanin Dakaru na Samson Jack a yankin Obonoma da misalin karfe 8.00 na Yammaci inda suka budewa dakaru wuta ba tare da sun yi aune ba.

'Yan Bindiga sun kashe Sojoji 3 a jihar Ribas
'Yan Bindiga sun kashe Sojoji 3 a jihar Ribas
Asali: Facebook

Baya ga sojoji uku da suka rasa rayukan su nan take yayin wannan mugun kwaton bauna, akwai kuma Dakaru da dama da suka samu munanan raunuka yayin da mai aukuwar ta auku kwatsam ba tare da sun farga ba.

Wata majiyar rahoto yayin ganawa da manema labarai na jaridar The Punch a jiya Lahadi ta bayyana cewa, Maharan haye kan Babura sun ci Karen su ba bu babbaka cikin kankanin lokaci kuma suka arce salin alin.

KARANTA KUMA: Dattijo mai shekaru 70 ya shiga da laifin Luwadi a jihar Jigawa

Sarkin gargajiya na al'ummar Obonoma, King Disrael Bob-Manuel, ya yi tur da wannan lamari da cewa yana da cikakken yakini Talakawan sa ba su da ikon sanya hannu cikin wannan muguwar ta'ada kasancewar su masoya zama lafiya da kwanciyar hankali.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel