Hukumar INEC tayi magana akan zargin sace takardun sakamako a Zamfara

Hukumar INEC tayi magana akan zargin sace takardun sakamako a Zamfara

- Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Zamfara ta karyata zargi da wassu jam’iyyun siyasa ke yi cewa an sace takardun sakamakon zaben gwamnoni

- Shugaban fannin ilimantar da masu zabe da sadarwa, Garba Galadima ya bayyana zargin a matsayin kanzon kurege

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), a jihar Zamfara ta karyata zargi da wassu jam’iyyun siyasa ke yi cewa an sace takardun sakamakon zaben gwamnoni.

Hukumar INEC tayi magana akan zargin sace takardun sakamako a Zamfara
Hukumar INEC tayi magana akan zargin sace takardun sakamako a Zamfara
Asali: Depositphotos

Shugaban fannin ilimantar da masu zabe da sadarwa, Garba Galadima ya fada wa jaridar Daily Trust cewa zarge zargen ba gaskiya bane illa kage.

Ya bayyana a ranar Laraba 6 ga watan Maris 2019, cewa za su kira jami’in zabe da ke yankin kananan hukumomi 14 don isar musu da kayan zabe, hade da takardun sakamakon zabe da takardun zabe.

KU KARANTA KUMA: Zargin mallakar takardar bogi: Bindow zai san makomarsa a yau

A wani lamari na daban, wani sabon rahoto daya bulla a ranar Litinin, 4 ga watan Feburairu ya bayyana cewa wata babbar kotun tarayya dake zamanta a titin kotu dake gyadi gyadi jahar Kano ta haramta ma Abba Kabir Yusuf kasancewa dan takarar gwamnan jahar Kano na jam’iyyar PDP.

Legit.ng ta ruwaito kotun ta yanke wannan hukunci ne duba da dimbin kura kuran da aka tafka yayin gudanar da zaben fidda gwani, kamar yadda wani dan takarar gwamna a PDP ya shigar gabanta.

Wannan hukunci na kotu ya kasance wani mataki ne na amsa bukatar da dan takarar gwamnan jahar Kano a inuwar jam’iyyar PDP, Al-Amin Little ya mika mata ne bayan ya shigar da kara gabanta, inda ya zargi PDP da yi masa rashin adalci a zaben fidda gwanin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel