Naka sai naka: Buhari ya antaya naira biliyan 55 don fara aikin hukumar kula da Arewa maso gabas

Naka sai naka: Buhari ya antaya naira biliyan 55 don fara aikin hukumar kula da Arewa maso gabas

Sabuwar hukumar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kirkiro da zai mayar da hankali wajen da yankin Arewa maso gabashin Najeriya,NEDC, zata fara aiki nan bada jimawa da kudin fara aiki da suka kai N55,000,000,000.

Legit.ng ta ruwaito sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Gida Mustapha ne ya tabbatar da haka a yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Lahadi, 3 ga watan Maris a garin Yola ta jahar Adamawa, inda yace ana kan gabar karshe na shirye shiryen fara aikin hukumar.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Babbar kotu ta kori surukin Kwankwaso daga takarar gwamnan jahar Kano

A jawabinsa, Boss ya bayyana cewa gwamnatin Buhari zata baiwa hukumar kudin fara aiki na naira biliyan goma, yayin da kasafin kudin hukumar na shekarar 2019 ya kai naira biliyan 45, sa’annan majalisar dattawa zata amince da sunayen yan majalisan zartarwa ta hukumar.

Haka zalika Boss ya bayyana wasu ayyukan da gwamnatin Buhari keyi na rage radadin mawuyacin halin da al’ummar yankin Arewa maso gabas suke ciki, inda yace gwamnatin na gina tagwayen hanyoyi daga Abuja zuwa Yola da kuma layin dogo na zamani da zai hada manyan biranen jihohin gaba daya.

Da yake tsokaci game da rawar da APC ta taka a zaben shugaban kasa daya gabata kuwa, Boss yace: “Bana jin APC ta taka mummunan rawa, a ganina APC ta yi kyan kai a zaben daya gabata, kada ka manta Atiku Abubakar dan jahar Adamawa ne.

“Kuma fa Atikun nan ya dade yana siyasa na tsawon shekaru 20, kuma ya taba zama mataimakin shugaban kasa na shekara 8, don haka nake ganin kamata yayi a yaba ma APC saboda bambancin kuri’un Atiku da Buhari bai wuce 30,000 ba.” Inji shi.

Daga karshe Boss yayi kira ga yayan jam’iyyar APC dasu kasance masu hadin kai, su zamto tsintsiya madaurin daya domin da haka ne kadai APC zata kai ga gaci a zaben gwamnoni da yan majalisun jaha da zai gudana a ranar 9 ga watan Maris.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel