Madallah: Ayade ya kaddamar da ma'aikatar samar da tsinken sakucen hakora a Cross Rivers

Madallah: Ayade ya kaddamar da ma'aikatar samar da tsinken sakucen hakora a Cross Rivers

- Gwamnan jihar Cross River, Farfesa Ben Ayade, ya kaddamar da wani sabuwar ma'aikata kirar zamani wacce za a rinka sarrafa tsinken sakucen hakora a jihar

- Ana sa ran ma'aikatar za ta rinka samar da tsinken sakucen hakoran guda miliyan 31 a kowacce rana

- A yayin da ya ke bukatar daukacin al'ummar jihar da su dukufa ainun wajen noman iccen 'Bamboo' wanda da shi ne ake samar tsinken sakucen hakora

Gwamnan jihar Cross River, Farfesa Ben Ayade, ya kaddamar da wani sabuwar ma'aikata kirar zamani wacce za a rinka sarrafa tsinken sakucen hakora a garin Ekori, karamar hukumar Yarkurr da ke jihar.

Ana sa ran ma'aikatar za ta rinka samar da tsinken sakucen hakoran guda miliyan 31 a kowacce rana.

Da ya ke jawabi, Ayade ya bayyana cewa "Wannan gwamnatin na kokarin samar da muhallin farfado da tattalin arziki wanda zai baiwa kowa damar samun bunkasar rayuwa a jihar. Ba zamu iya canja kasarmu ba har sai mun canja tsarin ma'aikatai da kasuwancin jihohinmu. Jihar Cross River ce ta farko da ta fara samar da irin wannan ma'aikata."

KARANTA WANNAN: Assha: Marin uwar miji da keta mata riga ya jefa wata mata cikin tsaka mai wuya

Madallah: Ayade ya kaddamar da ma'aikatar samar da tsinken sakucen hakora a Cross Rivers
Madallah: Ayade ya kaddamar da ma'aikatar samar da tsinken sakucen hakora a Cross Rivers
Asali: Twitter

"Ma'aikatar noma a 2016 ta koka kan yadda ake batar da akalla dalar Amurka miliyan 18 a kowacce shekara wajen shigo da tsinke sakucen hakora a Nigeria, wannan ne dalilin da ya sa muka yanke hukuncin samar da wannan ma'aikata domin dakile hakan."

Ayade ya bayyana cewa jihar Cross River ce jihar Nigeria ta farko da ta mallaki irin wannan ma'aikata, wacce za ta kasance karkashin kulawar 'yan jihar ba tare dasanya wani bakon haure ba, da zai bayar da damar samar da guraben ayyuka ga al'ummar jihar da ma sauran 'yan Nigeria baki daya.

A yayin da ya ke bukatar daukacin al'ummar jihar da su dukufa ainun wajen noman iccen 'Bamboo' wanda da shi ne ake samar tsinken sakucen hakora, gwamnan ya ce: "Iccen na da karancin lokacin tsirowa wannan ne ya sa ya ke cikin iyalin ciyayi kuma ya ke tsirowa da yawa.

"Ku noma iccen 'Bamboo' mai yawa; domin samun damar samar da tsinke sakucen hakora miliyan 31 a kowacce rana, wanda hakan zai samar da kudaden shiga masu yawa da kuma harkallar kasuwanci."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel