Zargin mallakar takardar bogi: Bindow zai san makomarsa a yau

Zargin mallakar takardar bogi: Bindow zai san makomarsa a yau

Wata baban kotun Babban Birnin Tarayya a Apo ta tsayar da yau a a matsayin ranar yanke hukuncin kara dake bukatar a soke gwamnan jihar Adamawa, Mohammed Jibrilla Bindow daga zaben gwamnoni da za a gudanar, bisa zargin gabatar da takardun shaida na bogi.

Da farko Justis Olukayode Adeniyi ya tsai da 1 ga watan Maris don yanke hukunci bayan lauyoyin jam’iyyu sun saurari kara da aka gabatar da jawabansu akan karan.

Har ila yau, a lokacin da aka gabatar da lamarin a ranar Juma’a, Justis Adeniyi ya roki jam’iyyu cewa ba a kammala shirye shiryen hukuncin ba.

Zargin mallakar takardar bogi: Bindow zai san makomarsa a yau
Zargin mallakar takardar bogi: Bindow zai san makomarsa a yau
Asali: Facebook

Yace a baya ya aika wa mai rigista a kotun da ya gabatar da lamarin ga jam’iyyu. Daga karshe ya tsai da yau a matsayin ranar gabatar da hukunci.

Wata kungiya mai suna, Incorporated Trustees of Kingdom Human Rights Foundation International, tayi zargin cewa Bindow ya gabatar da bayanan karya ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a Form CF001 da hukumar INEC ta bashi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugannin kudancin Kaduna sun yi barazanar barin PDP

Ya gabatar da takardan shaida na bogi dake nuna cewa yayi jarabawan West African Examination Council (WAEC), a watar Yuni, 1983.

Karar ta zargi gwamnan da bayyana takardun karatu na bogi ne don neman zabe na ofishin gwamnan jihar Adamawa a zaben 2019 na kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel