Yanzu Yanzu: Shugannin kudancin Kaduna sun yi barazanar barin PDP

Yanzu Yanzu: Shugannin kudancin Kaduna sun yi barazanar barin PDP

Gamayar kungiyar yan kudancin Kaduna (CSKN) sun yi barazanar barin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) idan har jam’iyyar ta gaza bayanin dalilin da yasa mafi akasarin shugabanninsu a jihar Kaduna suka fadi zabe a mazabunsu.

Da yake jawabi ga manema labarai a Kaduna, shugaban kungiyar, Dr. Yusuf Gandu Magaji yace abun damuwa me cewa dan takarar gwamnan PDP, alhaji Isa Ashiru da sauran shugabannin jam’iyyar sun gaza kawo mazabunsu a zaben majlisar dokoki da na shugaban kasa da aka kammala kwanan nan.

Yanzu Yanzu: Shugannin kudancin Kaduna sun yi barazanar barin PDP
Yanzu Yanzu: Shugannin kudancin Kaduna sun yi barazanar barin PDP
Asali: UGC

Shugabannin siyasa na yankin kudancin Kaduna sunce yan takarar PDP da sauran shugabannin jam’iyyar basu aminta da yadda sakamakon zaben ya zo ba a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu ba.

Yace akwai yaudara ta bangren shugabannin jam’iyyar daga wannan yankin.

KU KARANTA KUMA: Da dumi dumi: Babbar kotu ta kori surukin Kwankwaso daga takarar gwamnan jahar Kano

Kungiyar tayi barazanar janye goyon bayanta ga jam’iyyar idan har PDP ta gaza bayani kan rashin kokarinta a arewacin jihar sannan sun ba jam’iyyar sa’o’i 24 ta basu amsa.

Kungiyar tace za ta watsar da jam’iyyar idan ba ta bayar da amsa ba a cikin wa’adin sa’o’i 24 da ta diba mata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel