Zaben gwamnoni: Tinubu ya dakatar da gwamnan APC daga halartar kamfen a jihar sa

Zaben gwamnoni: Tinubu ya dakatar da gwamnan APC daga halartar kamfen a jihar sa

Abiola Ajimobi, gwamnan jihr Oyo, ba zai cigaba da halartar yakin neman zaben dan takarar gwamnan a karkashin inuwar jam’iyyar APC a jihar sa ba, kamar yadda majiyar mu ta bayyana ma na.

Ajimobi ya sha kaye a hannun jam’iyyar PDP a zaben kujerar sanatan jihar Oyo ta kudu da ya yi. Gwamnan ya samu kuri’u 92,579 yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Dakta Kola Balogun, ya samu kuri’u 105,720.

Wani lamari da ya kara bayar da mamaki shine yadda jam’iyyar PDP ta lashe zaben kujeru 4 daga cikin 5 na ‘yan majalisar wakilai da yankin na jihar Oyo ta kudu ke da su.

Faruwar hakan ne ta saka jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya karbi ragamar yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar ta Oyo a jam’iyyar APC domin ganin PDP ba ta kwace jihar ba.

Zaben gwamnoni: Tinubu ya dakatar da gwamnan APC daga halartar kamfen a jihar sa
Abiola Ajimobi
Asali: Depositphotos

Majiyar mu ta sanar da mu cewar yanzun haka Tinubu ya saye takarar tsohon gwamnan jihar, Alao Akala, domin kara wad an takarar APC, Bayo Adelabu, karfi sannan ya umarci gwamna Ajiomobi ya nesanta kan sa daga wurin yakin neman dan takarar.

DUBA WANNAN: Yadda APC ke shirin amfani da sojoji domin murde ma na zabe a Akwa Ibom –PDP

Wata majiyar jam’iyyar APC ta shaida wa majiyar mu cewar, “Tinubu ya fahimci cewar jama’ar jihar Oyo na jin haushin gwamna Ajimobi ne ba jam’iyyar APC ba.

“Abin tsoron shine zuwan Ajimobi wurin kamfen din Adelabu zai kara lalata damar da APC ke da shin a yin nasara a zaben gwamnoni da za a yi karshen mako.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel