Radadin shan kayi: PDP ta kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki don lalubo ma kanta mafita

Radadin shan kayi: PDP ta kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki don lalubo ma kanta mafita

Uwar jam’iyyar jam’iyyar PDP ta kasa ta kira wani taron masu ruwa da tsaki, jiga jigai da kuma manyan yayan jam’iyyar dake gudana a yanzu haka a babban ofishin jam’iyyar dake babban birnin tarayya Abuja.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito taron da aka shirya farawarsa tun da misalin karfe 12 na rana a ranar Litinin, 4 ga watan Maris bai fara ba har bayan karfe 1 na rana, makasudin taron shine tattaunawa tare da lalubo mafita mafi sauki ga jam’iyyar.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Babbar kotu ta kori surukin Kwankwaso daga takarar gwamnan jahar Kano

Ana sa ran taron zai mayar da hankali ne ga matakin da jam’iyyar ta dauka tare da dan takararta a zaben shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar wanda yayi fatali da sakamakon zaben shugaban kasar daya sha kayi, kuma ya dauki alwashin shigar da kara gaban kotu.

Idan za’a tuna, a ranar Talata data gabata ne shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar daya lashe zaben shugaban kasar daya gudana a ranar 23 ga watan Feburairu.

Sakamakon zaben da INEC ta sanar ya nuna shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zarce a mukaminsa bayan yan Najeriya sun bashi kuri’u miliyan goma sha biyar da dubu dari daya da casa’in da daya da dari takwas da arba’in da bakwai, 15,191,847.

Yayin da dan takarar shugabancin kasa daga jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya samu kuri’u miliyan goma sha daya da dubu dari biyu da sittin da biyu da dari tara da saba’in da takwas, 11,262, 978.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel