Bukarti yana shirin shiga Kotu da EFCC game da bidiyon Ganduje

Bukarti yana shirin shiga Kotu da EFCC game da bidiyon Ganduje

Audu Bulama Bukarti, wanda yana cikin manyan Lauyoyin da su ke neman gaskiya ta fito a game da zargin da ke kan gwamna Abdullahi Umar Ganduje da karbar rashawa yayi shirin shiga kotu da hukumar EFCC kwanan nan.

Bukarti yana shirin shiga Kotu da EFCC game da bidiyon Ganduje
Bulama Bukarti zai shiga Kotu da EFCC saboda zargin Ganduje
Asali: Twitter

Babban Lauya Bulama Bukarti mai kare hakkin Jama’a, yayi barazanar zuwa har gaban Alkali da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, bisa zargin sa da karbar dalolin kudi a matsayin rashawa.

Dama can Lauyan yace za su hadu a kotu da hukumar EFCC muddin aka ki ba shi sakamakon da aka yi a kan wasu fai-fai na bidiyo ana ikirarin gwamnan na Kano yana amsar rashawa daga hannun wasu ‘yan kwangila kwanakin baya.

KU KARANTA: Idan ‘Dan takarar Gwamna ya cancanta, ko a kowace Jam’iyya yake a zabe sa – Buhari

Yanzu wannan Lauya ya tabbatar da cewa kusan ya kammala duk wani shirin da ake bukata na kai EFCC gaban Alkali a dalilin rashin mika masa sakamakon binciken da tayi game da sahihancin bidiyon Ganduje da aka saki a baya.

Lauyan ya hakikance cewa ba zai bari wannan zargi da ke wuyan gwamnan na Kano ya wuce haka nan kurum ba tare da kotu ta dauki mataki ba. Yanzu haka dai Audu Bulama Bukarti yana karatu a Tony Blair Institute da ke Ingila.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel