Da dumi dumi: Babbar kotu ta kori surukin Kwankwaso daga takarar gwamnan jahar Kano

Da dumi dumi: Babbar kotu ta kori surukin Kwankwaso daga takarar gwamnan jahar Kano

Wani sabon rahoto daya bulla a ranar Litinin, 4 ga watan Feburairu ya bayyana cewa wata babbar kotun tarayya dake zamanta a titin kotu dake gyadi gyadi jahar Kano ta haramta ma Abba Kabir Yusuf kasancewa dan takarar gwamnan jahar Kano na jam’iyyar PDP.

Legit.ng ta ruwaito kotun ta yanke wannan hukunci ne duba da dimbin kura kuran da aka tafka yayin gudanar da zaben fidda gwani, kamar yadda wani dan takarar gwamna a PDP ya shigar gabanta.

KU KARANTA: Atiku ya bayyana dalilin da ya sa aka kama surukin sa da lauyan sa

Da dumi dumi: Babbar kotu ta kori surukin Kwankwaso daga takarar gwamnan jahar Kano
Kwankwaso da Abba
Asali: Twitter

Wannan hukunci na kotu ya kasance wani mataki ne na amsa bukatar da dan takarar gwamnan jahar Kano a inuwar jam’iyyar PDP, Al-Amin Little ya mika mata ne bayan ya shigar da kara gabanta, inda ya zargi PDP da yi masa rashin adalci a zaben fidda gwanin.

Daga karshe kotun ta umarci jam'iyyar PDP reshen jahar Kano da ta gudanar da sabon zaben fidda gwani daga yau zuwa ranar Asabar 9 ga watan Maris, kamar yadda mai Alkalin kotun mai sharia Lowis Allagao ya bayyana.

Sai dai a hannu guda kuma, uwar jam’iyyar PDP reshen jahar Kano ta fitar da wata sanarwa inda take musantan wannan hukunci, tare da bayyana cewa hukuncin kotun ya shafi jam’iyyar PDP ne banda dan takararta.

“Jam’iyyar PDP na janyo hankulan jama’a game da hukuncin da babban kotun tarayya ta yanke da cewa hukuncin ya shafi jam’iyyarmu ne kadai, banda dan takararmu, kuma tuni jam’iyyar ta daukaka kara.

“Kuma a yanzu haka dan takararmu na cigaba da shirye shiryen fafatawa a zaben gwamnoni dake tafe a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.” Inji shugaban riko na jam’iyyar PDP, Rabiu Suleiman Bichi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel