EL Classico: Matashi a Kano ya burma wa abokin sa wuka a ciki

EL Classico: Matashi a Kano ya burma wa abokin sa wuka a ciki

Wani mutum ya kasha abokin sa ta hanyar Burma ma sa wuka a ciki tare da raunata wani mutum guda bayan kamala wani wasan kwallon kafa a tsakanin kungiyar Barcelona da takwarar ta, Real Madrid, da aka yi a garin Madrid da ke kasar Spain.

Lamarin ya faru ne a unguwar Yakasai da ke karkashin karamar hukumar ‘Birni’ a cikin kwaryar birnin Kano.

A wasan da ake yi wa kirari da ‘El-Classico’, kungiyar Barcelona ta lallasa Real Madrid da ci daya mai ban haushi (1-0). Kamar yadda kungiyoyin biyu ke hamayya da juna, haka magoya bayan su a Kano da ragowar sassan Najeriya ke adawa da juna.

Musu mai zafi ya kaure a tsakanin Salisu Mohammad da abokin sa, Mujittapha Musa, bayan kamala wasan, lamarin da ya kai ga Salisu ya hallaka abokin sa, Mujittapha.

EL Classico: Matashi a Kano ya burma wa abokin sa wuka a ciki
EL Classico
Asali: Getty Images

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Kano, Abdullahi Haruna, ya shaida wa manema labarai cewar Salisu ya burma wa abokin sa Mujittapha wuka a ciki sannan ya raunata wani mutum guda.

DUBA WANNAN: Buhari ya fadi irin kalar mutanen da zai bawa mukami a zango na biyu

Kakakin ya kara da cewa an garzaya da Mujittapha zuwa asibitin Murtala inda likita ya tabbatar da cewar ya mutu. Dayan da ya samu rauni, ya na karbar magani da samun kulawa a asibitin.

Haruna ya ce sun kama mai laifin da wukar da ya yi amfani da ita wajen kasha abokin na sa. Kazalika, ya bayyana cewar za su gurfanar da shi da zarar sun kamala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel