Kungiyar kiristocin Najeriya reshen Arewa ta taya Buhari murna

Kungiyar kiristocin Najeriya reshen Arewa ta taya Buhari murna

Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), a jihohin Arewa 19 sun taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murna, ta kuma bukace shi da ya samar da hadin kai yayin gudanar da ayyukan gwamnati wannan karon.

A wani wasika zuwa ga shugaban kasar, mai kwanan wata 1 ga watan Maris, 2019, kungiyan CAN reshen Arewa ta ce nasarar Buhari a zabe ya kasance shaidar adalcinsa da nuna gaskiya a gwamnati.

Jawabin, wanda shugaban kungiyar, Yakuba Pam ya sa hannu, ya zo kamar haka: “Ka gudanar da gwamnati tare da hadin kai kamar yanda kayi alkawari a karkashin kudurin tafiyar da hadin kan kabilu daban-daban dake a Najeriya yanzu fiye da yanda aka samu hadin kai can baya.

"Muna rokon ka da ka cigaba da zama uba ga yan Najeriya kamar yanda muke kyautata zatton ganin cigaban kasa nan da shekaru 4 a karo na biyu da zaka yi a Ofis."

Kungiyar kiristocin Najeriya reshen Arewa ya taya Buhari murna
Kungiyar kiristocin Najeriya reshen Arewa ya taya Buhari murna
Asali: UGC

A wani jawabi irin wannan, Muhammad Abubakar, Sultan na Sokoto kuma shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), har ila yau ya taya Buhari murna, ya kuma yi kira ga yan adawa da su mayar da takobban su.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya bayyana dalilin da ya sa aka kama surukin sa da lauyan sa

Ko da yake kungiyar JNI bata ambaci sunan Atiku ba a jawabin da Khalid Abubakar ya sa hannu, babban sakatare, dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya fada a wannan matakin tunda shi kadai ne daga cikin yan takaran shugaban kasa da ya tafi kotu don kalubalantar sakamakon zabe.

A cewar jawabin, “har ila yau, muna kira ga yan siyasa masu takara a Najeriya, da sunan Allah, da su rungumi kaddara saboda a kowace gasa akan samu mai nasara da kuma mai asara."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel